Muhalli

TSAFTAR MUHALLI: Gwamnatin Kano Ta Bawa Kasuwar ‘Yan-lemo Wa’adin Kwanaki Uku

Written by Pyramid FM Kano

Gwamnatin jihar Kano ta bawa shugabanni kasuwar Na’ibawa ‘Yan-lemo a Karamar hukumar Kumbotso Wa’adin Kwanaki Uku su tsaftace kasuwar ko kuma a dauki mataki a Kansu.

Kwamishinan Muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan lokacin tsaftar Muhalli ta Kasuwannin da ma’aikatu harma da hukumomin gwamnati wacce ake gudanarwa a duk juma’ar karshen wata a Kano.

Kwamishinan ya bayyana rashin jindadin sa da yadda kasuwar ta kasance a cikin datti duk da yadda suka sanar da ziyarar da zasu kai, inda ya ce ma’aikatar Muhalli ta bawa shugabanni kasuwar Wa’adin Kwanaki Uku su tsaftace ce ta ko kuma a dauki mataki akan su.

“Ma’aikatar Muhalli ta bawa tsaftar kayayyakin abinci muhammancin saboda da yawa daga cikin su ba’a dafawa ake amfani da su, wannan yasa muke bawa tsaftar su muhammancin”, inji Getso.

Ku Karanta: Za Mu Tattauna da Shugabannin Kasuwar Sharada Don Masalahar Tsaftar Muhalli — Kabiru Getso

Kwamishinan ya bukaci sauran shugabanni kasuwannin a fadin jihar Kano da cigaba da kula da tsaftar Muhalli domin kula da lafiyar al’umma.

Haka zalika, kwamishinan ya yabawa shugabanni tashar mota ta Unguwa uku a Karamar hukumar Tarauni bisa yadda suka tsaftace dukkan sassan tashar inda ya bukace su da su cigaba da dabbaka tsarin domin kare lafiyar al’umma musamman matafiya.

A jawabinsa, shugaban Kasuwar ‘Yan-lemo Safiyanu Abdullahi ya nemi afuwar gwamnatin jihar Kano bisa yadda Kasuwar ta kasance a cikin datti duk kuwa da suna iya kokarin wajen tabbatar da tsaftar Muhalli.

Ku Karanta: Tsaftar Muhalli: An ci Tarar Tashar Motar Rijiyar Zaki Dubu 100, Kowacce Mota Dubu 10

“Muna sanar da mai girma kwamishinan kowanne lokaci muna iya kokarin mu na tsaftace wannan kasuwa, amma da ka share da an sake sauke wani kayan datti zai sake taruwa, amma muna bada tabbacin aiwatar da dukkan gyare-gyaren da aka bamu”, inji Safiyanu.

Shima Matemakin shugaban kungiyar direbobin mota na tashar mota ta Unguwa uku Abba Isa ya yabawa Gwamnatin jihar Kano dangane da yadda take kula da tsaftar Muhalli, inda ya bada tabbacin cigaba da kula da nufin tsare lafiyar abokan huldar su.

Leave a Comment