Muhalli

Tsaftar Muhalli: An ci Tarar Tashar Motar Rijiyar Zaki Dubu 100, Kowacce Mota Dubu 10

Written by Pyramid FM Kano

Ma’aikatar Muhalli ta jihar Kano ta ci tarar tashar mota ta Rijiyar Zaki da ke yankin Karamar hukumar Gwale Naira Dubu 100 sakamakon karya dokar tsaftar Muhalli.

Kotun tafi da gidan ka ta tsaftar Muhalli ce ta samu tashar motar tana gudanar da ayyukan ta a lokacin tsaftar Muhalli wanda hakan ya ci karo da dokar tsaftar Muhalli ta jihar Kano.

Da yake Yanke hukuncin, majistire Auwalu Yusuf Suleiman ya ce kotun ta sami shugabannin tashar da kuma direbobi da karya dokar tsaftar Muhalli, lamarin da ya sa ya umarcin a kunce Lambar motoci guda 7 wanda sune akan gaba wajen karya dokar tare da yiwa direbobin 7 tarar naira dubu 10 Kowannen su.

Da yake Karin haske, shugaban kwamitin koli na tsaftar Muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya bayyana takaicin sa kan yadda aka samu tashar da karya dokar.

Dakta Kabiru Getso wanda Kuma shine kwamishinan Muhalli na jihar Kano ya ce ma’aikatar Muhalli ba zata lamunci wata hukumar ko ma’aikata ko kasuwa ko Kuma dai-dai Kun mutane su rika karya dokar da Gwamnatin ta zartar da nufin cigaban al’umma ba.

Ku karanta: Mun Dasa Bishiyoyi Miliyan Hudu Cikin Shekaru Uku – Kabiru Getso

A yayin tsaftar Muhalli, kwamitin ya kuma ziyarci wani gurin zuba dake unguwar rafin Dan nana a yankin Karamar hukumar ungogo domin bincike gami da daukar matakin da ya dace akan gurin.

Haka Kuma bayan kammala tsaftar Muhalli, Dakta Kabiru Getso ya jagoranci cigaba da gudanar da ayyukan dashen bishiyoyi da ya kaddamar a makon da ya gabata domin yaki da matsalar dumamar yanayi da take addabar duniya Baki daya.

Kwamishinan ya kaddamar da dashen bishiyoyin a kan titin zuwa Gwarzo a kokarin sa ka kammala dashen bishiyoyin miliyan daya da Gwamnatin jihar Kano zata dasa a shekarar 2022 da muke ciki.

Daga nan yayi fatan al’ummar jihar Kano za su guji zuba shara a Magudanan ruwa, su Kuma guji sare bashiyoyi tare da tabbatar da kula da bishiyoyin da gwamnatin take dasawa da nufin kula da Muhalli dama cigaban al’umma.

Yayin tsaftar Muhallin, kotun tafi da gidan ka ta sami mutane 61 da laifin karya doka inda ta yi musu tarar naira dubu 185,600.

Leave a Comment