Da Dumi-Dumi

Tsaftace Kundin Shirin AGILE na Kano: Abubuwan Da Aka Cire Da Wanda Aka Kara

Written by Admin

Daga: SANI MAGAJI GARKO

ABUBUWAN DA AKA CIRE;

1. An cire dukkan hotunan da suka sabawa koyarwa addinin musulunci da al’adun mutanen Kano a cikin kundin, an maye gurbin su da wadanda suka dace ( Kano dress code).

2. An cire kalmar Gender-Based Violence, GBV (cin zarafin jinsi) an maye gurbintsa da ‘Safety and Security of children within and outside School’ wato (kare dalibai daga cutarwa a ciki da wajen makaranta), saboda kalmar GBV tana koyawa mata cewa, maza barazana ne a rayuwarsu.

3. An cire sadarar data baiwa mata yancin yin aikin gwamnati; “the right to work”.

4. An cire sadarar data baiwa yara ‘Yanci akan iyayen su.

5. An cire sadarar data baiwa mata ‘Yancin fita daga gidajen su a kowanne lokaci suka ga dama.

ABUBUWAN DA AKA KARA A KUNDIN;

1. Koyawa dalibai yadda ake alwala a aikace.

2. Koyawa dalibai yadda ake amfani da Aswaki da gawayi a wajen tsaftar baki.

3. Koyawa dalibai yadda ake tsarki a aikace.

4. Nusantar da dalibai cewa, lokacin da suke cikin jinin al’ada ba’a taba Al-Qur’ani mai girma, shiga masallaci, mu’amalar aure har sai bayan sunyi tsarki.

5. Koyawa dalibai sana’o’i da girmama iyayen su da mazajen su. Misali ‘Made in GGSS Unguwa Uku shoes & bags’ wato (kayayyakin da aka samar a makarantar sikandiren ‘Yan Mata ta Unguwa uku).

6. Za’a fassara kundin shirin AGILE zuwa yaren larabci da ajami.

An gudanar da taron karawa juna sani na kwana biyu (13-14 Disemba, 2023) wanda aka tsaftace kundin shirin AGILE a Kano.

A taron akwai wakilan Sarkin Kano da Karaye; wakilan Majalisar Malamai da Majalisar Limaman Juma’a da HISBAH da FOMWAN da ASSUS da Shugabannin Iyaye da lamamai gatan Makaranta (SBMC) da ma’aikatan ma’aikatar ilimin jihar Kano da shugabannin shirin AGILE da yan jaridu da sauran su.

Kwamishinan ilimin jahar Kano, Hon Umar Haruna Doguwa ya halarci gurin inda ya gabatar da jawabansa. Sannan ya jaddada godiyar sa ga malaman jihar Kano bisa gudummuwar su akan tarbiyar al’umma.

Allah ya taimaki gwamnatin jihar Kano.

Abba Rabiu Sarkin Fulani
Mamba Kwamitin Sake Duba a Kundin AGILE.
(Daga 13 – 14 Disamba, 2023)
16 Disamba, 2023.

Leave a Comment