Yanzu-Yanzu

Tinubu Zai Dakatar da likitoci masu zuwa kasashen ketare domin Neman aiki – Yakasai

 

Ibrahim Sani Gama.

Gamayyar kungiyoyin kiwon lafiya ta kasa dana jihohi tareda kugiyoyin dalibai sun gudanar da taron wayar da kai ga likitoci dangane da yadda za’a kawo karshen yawan fita kasashen wajen da likitoci ke yi a matsayin yin aiki.

Shugaban gamayyar kungiyoyin kuma, daya daga cikin jigajigan yakin neman zaben Dan takarar shugabancin Kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, wato, Dr. Umar Tanko Yakasai ne ya shirya taron wanda ya gudana anan Kano.

Umar Tanko Yakasai yace, an shirya taron ne saboda wayar da kan likitoci da dalibai a fannin kiwon lafiya yadda za’a lalubo bakin zaren matsalolin da suke faruwa da kawo karshen matsalar da take sanya likitoci da dama suke tafiya zuwa kasashen ketare domin yin aiki, maimakon zama a Kasar su gida Najeriya.

Yace, da yawa likitoci ‘yan asalin Najeriya suna gujewa zuwa wasu Kasashen ne sakamakon rashin biyansu hakkokinsu kamar yadda Kasashen ketare zasu biyasu, da rashin kayayyakin aiki da rashin ba da kulawa ta musamman ga ma’aikatan kiwon lafiya da suka taso a Kasar kuma suka yi karatu amma ba za su tsaya a Kasashen su tareda hidimtawa ba.

Ya kuma ce, kungiyoyin sun gudanar da taron ne, tareda hadin gwuiwar tsofaffin kwamishinonin kiwon lafiya na jihohi, musamman na jihar Legas wanda ya shugabanci ma’aikatar lafiya ta jihar a lokacin da Dan takarar shugabancin kasa, Asiwaju Ahmed Tinubu yana Gwamnan jihar, shi yasa yanzu Tinubun ya kudiri aniyar kawo karshen ficewar kwararrun likitoci daga Najeriya zuwa wasu kasashen da zummar neman aiki domin dogaro da kawunansu.

Umar Tanko Yakasai ya jaddada cewa,Tinubu ya sha alwashin magance irin wadannan matsaloli da suke damun fannin kiwon lafiya na kasar nan a halin yanzu, saboda yawan guduwa da ma’aikatan harkokin kiwon lafiya suke yi a fadin kasar nan, inda yace, wannan ba karamar matsala bace ga al’ummar Najeriya da bangaren lafiya na kasar nan.

Bola Tinubu yace da zarar ya zama shugaban kasa harkokin kiwon lafiya na daya daga cikin abubuwan da zai fara magancewa da samarwa likitoci ayyukan yi ta yadda za su takaita da fita zuwa kasashen ketare.

A jawabin shugabanin kungiyoyin dalibai a fannin harkokin kiwon lafiya Jibril Aliyu wanda Muhammad Murtala Abdullahi ya wakilta, ya bayyana matsalolin da suke sanya likitoci barin kasar nan da cewa, “rashin biyan albashi mai tsoka da rashin kayayyakin aiki, musamman na zamani dana kimiyya da fasaha suka haddasa hakan”.

Daga karshe kungiyoyin daliban sun yi kira ga Gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki a bangaren lafiya da su fito da wasu hanyoyin magance wannan matsala ta yawan ficewa da likitocin ke yi zuwa kasashen ketare domin yin aiki, da kuma dawo da wadanda suke zaune a can.

 

Leave a Comment