Yanzu-Yanzu

Tallafawa masu bukata ta musamman ita ce manufarmu – Gidauniyar Kanawa

By: Mukhtar Yahaya Shehu

Gidauniyar kanawa da ke tallafawa rayuwar masu bukata ta musamman ta jaddada kudurinta na cigaba da tallafawa wajen inganta rayuwars su.

Shugaban gidauniyar Malam Ibrahim Garba ne ya bayyana haka yayin taron koya wa masu bukata ta musamman sana’o’i Wanda hukumar kula da masu bukata ta musamman ta kasa ya shirya da hadin guiwa da wani kamfani Maizaman kan sa.

Ya ce manufar shirya taron shi ne domin tallafawa masu bukata ta musamman da sana’o’in dogaro da Kai a matsayin su na mutane kamar kowa.

Malam Ibrahim Garba ya ce gidauniyar Kanawa na aiki ba dare babu rana wajen kawo sauyi a rayuwar wadannan bayin Allah a fannoni daban daban.

“Muna wayar da kan kamfanoni masu zaman Kan su Kan yadda za su bai wa masu bukata ta musamman sama musu guraben aiki da Kuma tabbatar da aiwatar da dokar bai wa masu bukata ta musamman Kashi biyar cikin Dari na guraben aiki a matakin gwamnati”, Inji Ibrahim Garba.

Ya kara da cewa gidauniyar kanawa ta taka muhimmiyar rawa wajen kira ga gwamnatin jihar kano da majalisar dokokin jihar domin kafa hukumar kula da masu bukata ta musamman a matakin jiha Wanda tuni gwamna ya Sanya mata hannu bayan da ya zama doka.

Shi kuwa sakataren gidauniyar Sani Garba Dambatta ya bayyana cewa taron na hadin guiwa ya kunshi bai wa masu bukata ta musamman su 150 horo Kan sana’o’i da suka hadar da kiwon kaji da koyar da girki da gyaran jiki da kuma koyar da gyaran wayar hannu.

Sani Garba Dambatta ya ce cikin masu bukata ta musamman da suka amfana da Shirin akwai kurame da makafi da Guragu da zabiya da Kuma masu lalurar Laka.

Ya kuma jaddada kudurin gidauniyar ta Kanawa wajen hada hannu da kowa da kowa domin tallafawa rayuwar masu bukata ta musamman.

Leave a Comment