Siyasa

Talakawa Yakamata Ku Hidimtawa Ba Watsi Da Su Ba, Sakon Matawalle Ga Yan Siyasa.

Written by Pyramid FM Kano

Gwamnan jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle ya ja hankalin Yan Siyasa da su mayar da hankali wajen Hidimtawa Talakawan da suka zabe su ba suyi Watsi da su idan sunyi nasara ba.

Matawalle ya bayyana hakan ne a yayin taron bude babban ofishin ma kungiyar manyan Yan kasuwar jihar ta Zamfara masu lakabin “G7 Business Community” wanda suka sauya sheka daga jam’iyar PDP zuwa jam’iyar APC Mai mulkin jihar taron da ya gudana a shalkwatar kungiyar dake Nan Kano.

Ya ce matukar Yan Siyasa zasu rika Hidimtawa Talakawan da suka zabe su, basa bukatar Bada kudi domin a sake zabar su.

Ku Karanta: APC Zata Lashe Zabe a Kano Kafin 12 Rana — Faizu Alfindiki

A jawabinsa, babban Daraktan kungiyar G7 Honarabil Ibrahim Khalil Ahmad ya ce babu abinda ya ja ra’ayin su game da komawar su jamiyar APC ba fa ce karamci da gwamna zamfaran ya nuna musu.

Ya Kuma ce zasu bada gudun mowa domin tabbatar da Matawalle yayi nasara a zaben dake tafe.

Leave a Comment