Yanzu-Yanzu

Taimakawa marayu yana daga darajar Dan Adam – Ibrahim Khalil.

 

By: IBRAHIM SANI GAMA

An shawarci kungiyoyi masu zaman Kansu da mawadata, da su kara zage damtse wajen tallafawa marayu da marasa karfi a cikin Al’umma domin rage wahalhalu da fatara ta wannan zamanin.

Shahararren malamin nan Sheikh Ibrahim Khalil ne, ya ba da shawarar bayan kammala shan ruwa da Gidauniyar tallafawa marayu ta (C AND C) ta shirya Wanda ya gudana a Gidan Bambayya  dake nan jihar Kano.

Malam Ibrahim Khalil, yace, yana da muhimmanci da kyautatawa irin wadannan kungiyoyi da daidaikun mutane musamman masu hannu shuni domin ganin an taimakawa marayu da marasa hali wajen ganin su ma sun yi rayuwarsu kamar kowa.

Malam Khalil ya jadadda cewa, rashin aiwatar da tallafi irin wadannan, ya sanya Al’umma su tsinci kansu a cikin talauci da kin juna da gurbacewar marayu da
aka mutu aka barsu sakamakon watsi da aka yi da su.

Yace, akwai bukatar kungiyoyi, su yi amfani da wannan dama da yin koyi da Gidauniyar nan, wajen hada kawunansu da sanyawa kansu harajin da za su rika taimakawa marayu da zawarawa da kananan yara da aka mutu aka barsu, duba da Falalar dake cikin baiwa marayu taimako, musamman a lokacin da suke da bukatar haka.

Malam Ibrahim Khalil, ya kuma, bukaci ‘Yan jaridu da sauran kafafen yada labarai, da su taimakawa wannan Gidauniya wajen yada manufarta da ayyukan da take yi domin karawa sauran Al’umma karsashi da kwarin gwiwa na aiwatar da wannan tagomashi, kuma kabakin lada da zai zamewa Wanda suka yi Abin Alfahari Duniya da Lahira.

Yace, kasashen Duniya da dama, musamman na Larabawa, sun ci gaba da kawar da Talauci da yunwa ta hanyar taimakekeniya, musamman marasa hali da marayu.

A jawabinsa shugaban Gidauniyar na kasa Sunusi Garba Kalamaina, ya bayyana cewa, sun kafa Gidauniyar ne, domin taimakawa marayu da marasa hali wajen biya musu kudaden magani da raba Abinci da daukar Nauyin karatun marayu, a cikin jihohin Arewacin Najeriya.
Sunusi Garba yace, duk wadannan tallafe tallafe da kungiyar take yi, tana yi ne da karfinta da Dukiyarta ta hanyar tattara taimakon kudade da kayayyakin amfani da Al’umma ke bukata domin ganin marayu su ma sun ji dadin aiwatar da rayuwarsu kamar sauran Al’umma da ba marayu ba.

Shugaban Gidauniyar yace, ko kwanan nan, Gidauniyar ta je, gidajen marayu, Wanda ta samu damar tallafawa marayu da kayayyaki da abubuwan bukata na kudade da dama.

Ya kara da cewa, Gidauniyar tana zuwa Gidajen rediyo da Asibitoci domin daukewa masu bukatar taimako,Wanda wasu lokutan ma zaka ga kudin maganin da wani ko wata za su biya na magunguna ba ya wuce naira Dubu biyu ko biyar ba, amma sakamakon bashi dashi babu yadda zai yi.

Sunusi Garba, yace har yanzu Gidauniyar bata nemi taimakon wasu kungiyoyi ba, ko masu hannu da shuni, saboda duk Wanda yake bukatar tallafawa marayu da marasa hali, kofarsu a bude take a duk inda suke ba za su rasa mabukata ba.

Haka zalika yace, suna yin hakan ne, saboda karawa sauran Al’umma da kungiyoyi karfin gwiwa da wayar da kan jama’a ta hanyar shiga gidajen rediyo da kafafen sadarwa domin fahimtar da Al’umma, inda yace, wannan Gidauniyar Al’umma da yawane suka kafata a fadin kasar nan domin agazawa bayin Allah.

Shugaban ya bayyana cewa, Gidauniyar ta kwashe Shekaru da dama tana gudanar da irin wannan taron shan ruwa ta hanyar gayyatar Alumma da yawa domin kara karfafa Alaka da zumunci a tsakanin ;ya;yan kungiyar da ma wadanda ba yankungiyar ba.

Al’umma da dama ne suka samu halartar taron shan ruwan fadin jihar kano da sauran jihohin waje, domin ganin an gudanar da wannan shan ruwa da Gidauniyar ta saba shiryawa Duk shekara a cikin watan Azumin watan Ramadana.

(COV/Ibrahim Sani Gama Pyramid Radio.)

Leave a Comment