Da Dumi-Dumi Kasuwanci

Singa: Sauye – sauyen Inganta Kasuwar Da Bunkasa Harkokin Ta (SIMADA)

Written by Pyramid FM Kano

Daga: IBRAHIM SANI GAMA

Kungiyar ‘yan kasuwar Singa ta jihar Kano, ta jaddada kudirinta na kara bunkasa kasuwar yadda ya kamata domin ciyar da kasuwanci da kasuwar gaba.

Shugaban Kungiyar na jihar Kano Barista Junaidu Mohammed Zakari ne ya bayyana haka a lokacin zantawa da manema labarai jim kadan bayan kaddamar da sabon Shugabanci na riko wanda ya gudana a harabar kasuwar.

Shugaban yace, sabon shugabanci zai aiwatar da ayyukan ci gaba da za su inganta kasuwar da sauye-sauyen da suka hadar da samar da magudanan ruwa da wutar lantarki domin a ci gaba da kasuwacin dare da tallafawa matasan kasuwar Singa da suke da bukatar komawa karo karatu da kuma samar da tsaro domin kare dukiyoyin al’umma.

Barista Junaidu ya bayyana cewa, za su samar da tallafi daga gwamnati ga kananan ‘yan kasuwa da basu da karfin jari ta hanyar hada hannu da masu ruwa da tsaki na ma’aikatar kasuwanci da ciniki ta jihar Kano da ma sauran abubuwan ci gaba na bunkasa harkokin kasuwanci da farfado da tattalin arzikin jihar Kano.

A nasa bangaren, mataimakin kungiyar na Kwanar Singa Alh. Bashir Yusuf Abdullahi ya bayyana cewa, makasudin kafa wannan kungiya shine, domin a samu zaman lafiya da ci gaba tsakanin manya da kananan ‘yan kasuwa da ma su kansu leburori.

Alh. Bashir Yusuf yace, dangane da haka ne kungiyar Kasuwar ta dauko shugabanci daga kowanne gida na kasuwar ta Singa domin a samu daidaito na baiwa kowanne bangare hakkinsa da tabbatar wakilci.

Mataimakin Kungiyar Kasuwar, ya yabawa Dattawa na kasuwar da suke bayar da gudunmawa wajen bunkasar harkokin kasuwanci yadda ya kamata.

Yace, kungiyar Kasuwar ta samar da motar kashe gobara domin kare iftila’in gonara wajen kawo dauki cikin gaggawa wanda ba fatan hakan ake ba.

Bashir Yusuf ya godewa kamfanonin da suke matukar bayar da gagarumar gudunmawa a kasuwar Singa daga lokaci zuwa lokaci na ganin an bunkasa harkokin kasuwanci.

Shi ma a jawabinsa, shugaban kamfanin Mamuda Hassan Ahmed da takwaransa na kamfanin Aspira, sun bayyana jin dadinsu bisa wannan kungiya da ‘yan kasuwar ta Singa duba da kyakykyawar alaka da suke ta samu daga wurin ‘yan kasuwa, musamman ta hanyoyin kasuwanci.

Hassan Ahmed ya jaddada kudirinsu na ci gaba da mu’amulla tsakanisu ta hanyar kasuwanci da zumunci a ko da yaushe.

Al’umma da dama ne suka halarci taron da suka hadar da: Wakilin Gwamnan Kano da wakilin Maimartaba Sarkin jihar Kano Alh. Ibrahim Ado Bayero da Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Kano da dai sauransu,

Haka su ma sun yabawa Dattijan wannan Kungiya, jajircewar da suka yi na ganin an samar da kasuwar Singa sabuwa, wanda daga cikin Dattawan Kungiyar akwai, Alh. Salisu Sambajo da Alhaji karami da Alh. Adakawa da Alh. Dangwangola da Alh. Sani Isah da dai sauransu wajen ba da gudunmawa na ganin cewar Kasuwar ta Singa ta zama abar kwatance a Nahiyar Afirka, domin yin gogayya da sauran kaduwannin Duniya kasancewar Kano ita ce cibiyar Kasuwanci a Kasar nan baki daya.

 

Leave a Comment