Yanzu-Yanzu

Shugaba Tinubu Ya Dauki Hanyar Inganta Makarantun Tsangayu

Written by Admin

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu

An bayyana nadin da Shugaban Kasar Najeriya ya yi wa Ritaya Janar Lawal Jafaru Isa Kano da Dr. Sani Muhammad Idris Yobe da cewa abu ne da zai Kara inganta harkar ilimin addinin Musulunci da ilmin Tsangayu a Kasar nan.

Jawanin hakan ya biyo bayan wata sanarwar da kungiyar Samarin Tijjaniyya ta Kasa ta fitar mai dauke dasa hannun Babban Sakataren Kungiyar na Kasa Shehu Tasi’u Ishaq da Babban Jami’in yada Labaran Kungiyar na Kasa Abubakar Balarabe Kofar Naisa.

Sanarwar ta ce idan aka yi la”akari da irin gudunmawar da wadannan mutane biyu suka bayar wajan cigaban addinin Musulunci da inganta makarantun tsangayu Shugaba Tinibu ya yi namijin kokari da hangen nesa wajan basu wadannan mukamai.

Sai dai kuma Kungiyar Samarin Tijjaniyyar ta Kasa taja hankalin wadanda aka bawa wadannan mukamai da su yi aiki tsakaninsu da Allah bisa amana da gaskiya kamar yadda aka san su tare da nuna rashin banbanci ko bangaranci domin ciyar da Kasar nan gaba.

Sanarwar ta yaba wa Shugaba Ahmed Bola Tinibu bisa yadda ya ke nada mukamai ta hanyar zabo jajirtattu da kuma ajiye kowa a gurbinsa wanda ya kware a fannin da yake domin gudanar da aikin cigaban Kasa.

Daga nan Kungiyar Samarin Tijjaniyyar ta yi kira ga ‘yan Najeriya su cigaba da yi wa wannan Kasar aduu’ar samun zaman lafiya da karuwar arziki da dorewar tattalin arziki da kuma samun cikakken tsaro musamman a wasu jihohi da ake fama da tabarbarewar tsaro.

Leave a Comment