Yanzu-Yanzu

Shiga yajin aiki makarkashiya ne da rashin tausayin Dalibai -Farfesa Bashir

By: KABIR GETSO

Shugaban kwalejin ilimi da fasaha ta Tarayya dake Bichi (Federal College of Education Technical Bichi) Farfesa Bashir Muhammad Fagge, yace Shiga yajin aiki da kungiyar Malaman kwalejin sukai wata makarkashiya ce da rashin tausayin Dalibai.

Ya bayyanna hakan ne lokacin da yake jawabi ga manema Labarai dangane da yajin aikin da Kungiyar ta Shiga a sakamakon wasu zarge zarge da suka bayyanna.

Farfesa Bashir yace Sun aiko da Takarda ga Hukumar Kwalejin a ranar 5 ga watan da muke ciki inda kuma suka shiga yajin aikin tun a ranar 6 ga watan da muke ciki ba tare da bada lokaci an zauna domin duba Bukatunsu ba,don haka wannan kadai ya isa ya bayyanna cewa akwai wata makarkashiya da ake so a kulla don bata masa suna.

farfesa Bashir Fagge yace kasa da watanni 2 ya rage masa na wa’adin Shugabantar kwalejin inda ya kwashe Shekaru Takwas yana Shugabantar kwalejin tare da aiki tukuru don ciyar da kwalejin gaba.

Wasu daga Cikin irin manyan Nasarorin da ya kwalejin ta samu sun hada da Tarewa a mazaunin kwalejin na dindindin da samar da manyan gine gine da dibar sabbin ma’aikata sama da Dubu daya da kuma sauran manyan ayyuka da dama.

Ya kara da cewa yanzu haka Takardar Daukar Sabon Shugaban kwalejin tana gaban Shugaban kasa inda zai karbi ragamar shugabancin nan da kankanin lokaci. Don haka kamata yayi su fito da irin wannan Nasarorin da kwalejin ta samu maimakon zarge zargen da basu da tushe bare makama.

Farfesan yace Duk wasu hakkokinsu da suka shafi kudade ana bin duk matakan da Yakama domin basu hakkokinsu, Misali kamar alawus na Teaching practice ya zo kwalejin ana bawa malaman Dubu tara inda daga bisani ya maida su Sama da dubu 30,don haka ya kamata suyi adalci,kafin aiwatar da shirin yajin aikin.

Kazalika Farfesan yayi kira ga Daliban da su kalli cigaban kwalejin da kuma Karatun Daliban sama da bukatun kansu don ciyar da Jihar Kano Dama kasa baki daya,ya kuma yi kira da Dalibai dama iyayen Dalibai da su kwantar da hankalinsu,komai zai cigaba da wakana yadda ya kamata a Kwalejin

A cikin Makon nan ne dai Shugaban Kungiyar malaman Kwalejin Dr Husaini Yahaya Pine ya sanar da shirinsu na shiga yajin aikin bisa wasu zarge zarge da ya bayyanna.

Leave a Comment