Da Dumi-Dumi

Sarkin Kano ya ziyarci tsohon shugaban kasa Buhari

By: MUKHTAR YAHAYA SHEHU

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, JP ya taya Tsohon shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari murnar kammala wa”adin mulkinsa lafiya.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya ziyarci tsohon shugaban kasar ne a gidansa da ke Daura domin yi masa fatan alheri sakamakon wa’adinsa da ya kare a zangon mulkinsa.

Cikin sanarwa Mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran masarautar Kano Alhaji Abubakar Balarabe Kofar Na’isa Mai Martaba Sarkin na Kano ya ce a mulki irin na babbar kasa Tarayyar Najeriya kuma Buharin ya yi shekara takwas yana gudanar da mulki abun a tayashi murna ne kamar yadda ya fara lafiya kuma ya kammala lafiya.

Ya ce a tsawon shekara Takwas dole a yi dai dai ko akasin haka, a don hakane ya yi fatan samun rahama da yafiyar ubangiji Allah.

Leave a Comment