Da Dumi-Dumi Labaran Jiha

Sarkin Kano Bayero Ya Taya Gwamna Abba Murnar Nasara A Kotun Koli

Written by Admin

Daga: MUKHTAR YAHAYA SHEHU 

Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya taya gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf murnar nasarar da ya samu a kotun koli.

Sarki Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce hukuncin kotun koli nuni ne na zabin mutane da kuma dimokuradiyya da kuma shugabanni na kwarai da masu biyayya ga abin da masu zabe za su yi.

A cikin sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na masarautar Kano Abubakar Balarabe Kofar na’isa Mai martaba Sarkin ya yabawa al’ummar jihar Kano bisa zabin da ya dace wanda zai tabbatar da ci gaba da tsare-tsare na cigaban jihar.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi addu’ar Ubangiji Allah ya kare shi daga makiya na zahiri da badini, ya kuma ba shi kwarin guiwar cika alkawura da kuma gudanar da ayyukansa cikin himma da nasara.

Leave a Comment