Yanzu-Yanzu

Sarkin Kano Alhaji Aminu ya dawo Gida bayan kammala Umrah

 

By: MUKHTAR YAHAYA SHEHU

Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya sauka a filin saukar jiragen sama na kasa da ksa na Aminu da ke nan Kano tare da dan uwansa Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero da Mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji Dr. Rilwanu Sulaiman Adamu.

A lokacin ziyarar aikin Umrah a kasa mai tsarki Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yana tare da Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Cikin sanarwa Mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran masarautar Kano Alhaji Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ta ce Mai Martaba Sarkin Kano ya sami tarba daga Hakimansa da sauran manyan ‘yan Kasuwa tare da al’umar gari wadanda sukayi dafifi akan titi suna lale marhabun da dawowar uban kasa.

Leave a Comment