Labaran Jiha

SARKIN DILLALAN KANO: An Nada Mukamin Sarkin Dillalin Kano

Written by Admin

Daga: ADAMU DABO

Samar da wakilci a dukkanin shiyyoyi zai taimaka wajen gudanar da jagoranci cikin nasara da kawo cigaba a jihar Kano.

Sarkin fawan Kano Alh. Isiyaku Alin Muli ne ya bayyana haka alokacin da yake zantawa da manema labarai a wajen bikin nadin wakilai da Sarkin Dillalan kano yayi a Fadarsa dake kofar ruwa karamar hukumar Dala.

Sarkin fawan yace nadin da sarkin dillalan yayi na wadanda zasu taimaka masa don gudanar da ayyukansa cikin sauki zai taimaka kwarai wajen dakile shigowar bata gari cikin jihar Kano

Shima anasa jawabin daya daga cikin masu rabauta da mukaman da aka nada wato makaman sarkin dillan kano Alhaji Naziru Tijjani ya godewa Allah bisa nada shi a matsayin makaman sarkin dillan kano tare da fatan zasu kawo gyra a harkar Samar da filaye a fadin kano

Da yake nasa Jawabin Sarkin Dillalan Jihar Kano Alh Mustapha Abdullahi Arrow yace wannan nadin da Yayi zai taimaka masa kwarai wajen gyara harkar dillanci da bada hayar gidaje a jihar Kano.

Ya kuma ja hankalin wadanda suka rabauta da wadannan mukamai dasu ji tsoron Allah wajen gudanar da aikinsu.

Daga bisani ya godewa gwamnatin Jihar kano da ayyukan da take gudanarwa a jihar ya kuma jinjinawa masarautar kano bisa jagorancin Sarkin kano Alh Aminu Ado Bayero da irin karfafa musu gwiwa da kuma basu shawara da take wajen gudanar da ayyukansu taron ya samu halartar Alumma daban daban daga cikin jiha dama kasa baki daya.

Leave a Comment