Labaran Jiha

Sama Da Dalibai 1.2M Suka Amfana Da Shirin Fadada Makarantun Sakandare a Kano – Shugaban AGILE

Written by Admin

Daga: Sani MAGAJI Garko

Shirin bunkasa ilimin ‘ya’ya mata a jihar Kano AGILE ya ce sama da yara Mata Miliyan daya da dubu dari biyu ne suka amfana da Shirin baya ga fadada makarantun sikandiren ‘Yan Mata harma da na maza.

Shugaban shirin a Jihar Kano Nasiru Abdullahi Kwalli ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai.

Nasir Kwalli ya ce, makasudin shirin shine magance matsalolin da suka addabi ilimin ‘ya’ya mata da makarantun Sakandare, wadanda galibi ke fuskantar matsaloli kamar rashin isassun kayan koyo da koyarwa a makarantu da ruwan sha da kuma tsaftar muhalli.

Kwalli ya kuma kara da cewa, shirin AGILE yana samun ci gaba wajen inganta da samar da ilimi ga yara mata masu tasowa a yankunan karkara.

Ya kuma ce, idan ana son ganin an samu ci gaba a cikin al’umma, to sai anfara da gyaran tarbiyyar ‘ya’ya mata domin su ne suke tarbiyar al’umma.

A cewars, ya zuwa yanzu an gyara makarantun sakandire 1,228 kuma ana ci gaba da Gina wasu sabbi a makarantun.

Ya kuma ce kimanin dalibai 1,269,673 ne suka amfana kai tsaye da ayyukan AGILE da fadada makarantu.

Shirin AGILE dan a samar da shi ne don Inganta ilimin ‘ya’ya Mata musamman a jihohin da suke da yawan yaran da basu zuwa makaranta wanda bankin Duniya da ma’aikatar ilimi ta tarayya da ma ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ke daukar nauyin sa.

Leave a Comment