Yanzu-Yanzu

Sakacin iyayene ke haifar da Rashin Tarbiyya da aikata miyagun laifuka – Salisu Kutam

By: KABIR GETSO

DARAKTAN Hukumar wayar da kai da fadakar da jama’a na Jihar Kano (N.O.A)
Alh Salisu Waziri Kutam ya bayyana cewa sakacin iyayene ne ke haifar da matasa masu aikata miyagun laiifuka a Jihar nan.

Ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da mane ma labarai a Ofishinsa, yace babu yadda za’ai iyaye suyi sarere da ‘ya’yansu ba tare da wata kulawar kirki ba ta fuskar Ilimi, suttura abinci da wajen kwana, wannan wata babbar barazana ce da ka iya haifar da miyagun laifuka ga matasan.

Wazirin Kutama ya kara da cewar kamar yadda Hausawa kance icce tun yana karami ake tankwara shi to ya zama wajibi ga iyayen su tanadi duk wasu bukatu na ‘ya’yan nasu kafin ma su mallaki hankalinsu domin hakan ne kawai zai magance irin wadannan matsaloli da matasan kan jefa kansu a ciki.

Kazalika ya yi kira ga Gwamnati da aauran hukumomin tsaro da Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) da su rubanya kokarinsu na fatattakar masu fataucin miyagun kwayoyin domin suna taka muhimmiyar rawa wajen jefa matasan irin wadannan miyagun halaye.

A hannu guda kuma su kuma al’ummar unguwanni da su bada hadin kai ga jami’an tsaro da sauran hukumomi wajen kai rahoton duk wasu bata gari da ka iya zama barazana ga al’umma domin hukuntasu daidai da abinda suka aikata, tare da kira ga masu hannu da shuni da su kara himma wajen taimakawa marasa karfi.

Sannan yayi kira ga al’umma da a cigaba da addu’a domin cigaban dorewar zaman lafiya ga al’ummar Jihar Kano dama kasa baki daya.

Leave a Comment