Da Dumi-Dumi

Sabon kwamishinan Ilmi Mai zurfi ya kama aiki

By: MUKHTAR YAHAYA SHEHU

Sabon Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi mai zurfi Dr. Yusuf Ibrahim Kofar Mata ya ce gaskiya da rukon amana da jajircewa sune ginshikin ci gaba.

Kwamishina ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi ragamar tafiyar da ma’aikatar jim kadan bayan gwamna Engr. Abba Kabir Yusuf ya jagoranci rantsar da sabbin kwamishinan a fadar gwamnatin jihar.

Cikin sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in yada labaran ma’aikatar Sunusi Kofar Na’isa Dr. Kofar Mata ya jaddada cewa gwamnatin Engr. Abba Kabir Yusuf ta zo ne domin ta samar da abubuwan kyautata rayuwar jama’ar jihar tare da mai do da darajar ilimi.

Kwamishinan ya bada tabbacin bunkasa ilimi mai zurfi ga matasan jihar nan tare da inganta manyan makarantu mallakin gwanatin Jihar Kano.

Ya jaddada kudirinsa na tafiya kafada-da-kafada da ma’ikatan ma’aikatar Ilimi mai zurfi da kuma manyan makarantun ilimi gami da barin ofishinsa a bude domin karbar shawara domin cigaban ilimi.

Haka kuma Dr. Yusuf Kofar Mata, ya ce gwamnati na duba yiwuwar dawo da tsohon sunan Jami’ar Yusuf Maitama Sule zuwa sunanta na ainihi wato Northwest. Ya godewa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa nada shi a matsayin Kwamishina tare da yabawa tsohon gwamna Dr. Rabiu Musa Kwankwaso bisa gwagwarmayar kawo sauyi a siyasar Jihar Kano.

Da yake jawabi a madaddin ma’aikata, Babban Sakatare Alh. Dahiru Adda’u, ya nuna farin ciki da samun Dr. Kofar Mata a matsayin Kwamishina na Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi ya kuma bayar da tabbacin samun hadin kan ma’aikata domin samun nasara.

Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kura da Garun Malam da Madobi, Alh. Yusuf Datti Umar da tsohon Minista Dr. Bala Borodo da Barayen Karaye Engr. Ibrahim Karaye na daga cikin wadanda sukai jawabai, bisa rakiyar daruruwan magoya baya maza da mata.

Leave a Comment