Addini

Rikicin Shugabanci Ya Hana Sallar Juma’a A Masallaci Marigayi Dr. BUK

Written by Pyramid FM Kano

Rikicin jagoranci ya tilasta rashin yin sallar Jumu’a a Masallacin Darul Hadith na marigayi Dakta Ahmad Ibrahim BUK.

Tarzoma ta kaure a Masallacin ne lokacin da sabon liman zai hau Mumbari don soma huɗuba, inda wasu fusatattu suka janyo rigarsa ta baya don nuna ƙin amincewa da shi, lamarin da ya kawo rikici.

Tuni aka rufe masallacin tare da baza jami’an tsaro a kofa da kewayensa.

Ku Karanta: Muna Bukatar Tallafin Gwamnatin Kano Inji Kungiyar Masu Kayar Gwari

Freedom Radio ta rawaito cewa bangarorin biyu dai sun ziyarci shalkwatar ƴan sanda da ke Bompai domin sasantawa.

Rahotanni sun bayyana cewa al’amura sun soma komawa daidai a unguwar Tudun Yola da ke Kano.

Leave a Comment