Labaran Jiha

RFI Hausa Zata Kulla Alaka da Masarautar Kano

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Muktar Yahaya Shehu

Sashen Hausa na Radio France International (RFI) ya ce zai Kulla Alaka da Masarautar Kano domin cigaban harshen Hausa da kuma cigaban al’adu.

Shugabar sashen Sophie Bouillon ce ta bayyana hakan a fadar Masarautar Kano a cigaba da ziyarar da ta kawo Kano.

Cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na Masarautar Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya fitar ta ambato misis Bouillon na cewa ta ga yadda taga abubuwan tarihi da al’adu a masarautar ta Kano ya tabbatar da cewa tsohuwar Masarauta ce da ta rike al’ada da ababan tarihi.

Shugabar sashin Hausa ta gidan Radio France ta ce zatayi duk abunda ya kamata wajen cigaba da kulla kyakkyawar alaka da yada manufofi da al’adun gargajiya na Masarautar ta Kano.

Ku karanta: Za Mu Cigaba Da Bada Gagarumar Gudun Mowa a Bangaren Lafiya — Aminu Ado

Ta yabawa Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero bisa irin hadin kai da goyon baya da yake baiwa kafofin yada Labarai na cikin gida da kuma na kasashen waje.

Da suke zagayawa da ita wasu bangarori na fadar, Babban Sakataren Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Haruna Kwaru da kuma Sakataren yada Labarai na masarautar Kano Abubakar Balarabe Kofar Naisa sun godewa shugabar Sashin Hausa ta gidan Radio France RFI Sophie Bouillon bisa ziyarar data kawo masarautar.

Inda kuma suka bata tabbacin hadin kai da goyon baya domin cimma kudurce-kudurcen da tazo dashi domin samun Nasarar da ake bukata.

Leave a Comment