Labaran Kasa

Rejista Da Karbar Katin Dan Kasa Na Da Matukar Muhimmanci — Aminu Ado

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Muktar Yahaya Shehu

Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yace yin Rajista da Karbar Katin Dan kasa yana da matukar muhimmanci a wajen al’ummar kasar nan duba da yanda al’umma suke yawan tafiye tafiye zuwa kasashen waje.

Sakataren yada labaran masarautar Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya aikowa Radio Nigeria Pyramid FM Kano.

Sanarwar ta ce mai martaba sarkin ya bayyana haka ne lokacin da Shugaban Hukumar Kula da Katin Dan Kasa wato National Identity Management Commission (NIMC) suka kawo masa ziyara a fadarsa.

Mai Martaba Sarkin, wanda Madakin Kano ya wakilta yace Masarautar Kano zata mara musu baya wajen fadakar da dagatai da masu unguwanni don sanin mahimmanci katin Dan kasa.

Ku karanta: Zamu Sauya Tsarin Koyar da Sana’o’i da NUC ta zo da shi Don Samarwa Matasa Aiki — Farfesa Kurawa

A nasa jawabin, shugaban Hukumar ta NIMC Alhaji Abdullahi Ahmed ya ce sunje fadar Masarautar Kano ne don neman goyon bayan masarauta don samun nasarar gudanar da aiyukansu don jama’a su fahimcin muhinmancin Katin Dan kasa.

Masarautar ta Kano daga ta tabbatar da cewa zata basu hadin kai da goyon baya wajen fadakar da al’umma kan mahimmaci katin Dan kasa yake dashi.

Leave a Comment