Da Dumi-Dumi Labaran Jiha

Ramadan: Kungiyar HONIA ta Tallafawa Marayu Da Kayan Abinci Da Na Sawa

Written by Admin

Daga: Sani Magaji Garko

Kungiyar cigaban Unguwar Hotoro a yankin Karamar Hukumar Nassarawa wato HONIA ta Tallafawa Marayu da gajiyayyu da kayan abinci da kuma Kayan atamfofi domin rage musu radadin halin da ake ciki na matsin rayuwa.

Da yake Kaddamar da rabon kayan, shugaban kungiyar Malam Muhammad Kabir Usman ya ce tallafin wanda aka dauki tsawon lokaci ana yinsa yana mayar da hankali domin tallafawa Marayu da gajiyayyu a cikin alumma musamman a watan Ramadan.

Ya ce, an tallafawa Marayu da gajiyayyun su goma 10 da Taliya Katan daya-daya da Atamfofi ko Yaduka kowannensu domin gudanar da azumin watan Ramadan da bukukuwan Sallah cikin farin ciki da annashuwa.

“Muna raba wadannan kayayyaki ne Karkashin jagorancin wannan kungiya ta HONIA wacce take a Kan layin Garsan Fulani a unguwar Hotoron Arewa, wannan tallafi an same shi ne daga gudun mowar da alummar wannan unguwa suka bayar Allah ya saka musu da alkhairi, dama anayi a baya, a wannan karon an sake bijoro da shi ne sakamakon matsin rayuwa da alumma suka sami kansu a ciki,” inji shugaban HONIA.

Daga nan ya yabawa al’ummar da suka bada gudun mowar tare da kwamitin da aka nada wanda ya karbo tallafin don rabawa mabukata.

A nasa bangaren shugaban Kwamitin karbo tallafin Alhaji Sanusi Malumfashi ya ce dama an samar da kwamitin ne domin karbo tallafin daga Mawadatan dake tsakanin alumma a unguwar don bawa Marayu da kuma gajiyayyu.

Sanusi Malumfashi ya bukaci shugabanni da mawadata da gwamnatoci da su rika tallafawa na kasa da su musamman a watan Ramadan don samun falala a gurin Allah.

Da suke karbar tallafin, Iyalan Marigayi Malam Sabo Direba sun bayyana farin cikinsu tare da yabawa Kungiyar ta HONIA bisa kula da su bayan rasuwar mahaifinsu.

Leave a Comment