Siyasa

Zaben Kungiyar Yan Jaridu Na Pyramid: Za Mu Samar Da Kwamitin Da Zai Aiwatar da Manufofin Mu — Aminu Kwaru

Written by Pyramid FM Kano

Sabon shugaban kungiyar ‘Yan Jaridu ta Kasa reshen gidan Radiyon Tarayya Pyramid FM Kwamared Aminu Abba Kwaru ya Sha Alwashin Samar da kwamitin da zai aiwatar da dukkan Manufofin sa.

Aminu Kwaru ya bayyana hakan ne lokacin da yake rantsuwar kama aiki a Matsayin sabon shugaban kungiyar na Pyramid Radio.

Ya ce zasu tabbatar da Samar da tsare-tsare da zasu kawo cigaban harkokin yada labarai da sashen labarai da al’amuran yau da kullum dama walwalar ‘ya’yan kungiyar.

Ya godewa wandanda suka zabe shi da ma wadanda basu zabe shi ba musamman daraktan yakin Neman zaben sa Ibrahim Sani Gama.

“Zabe ya kare, saboda haka muna fatan sauran wadanda basu yi Nasara ba zasu zo muyi tafiya daya domin cigaban wannan gida”, inji Aminu Kwaru.

Ku Karanta: Ku Guji Shiga Bangar Siyasa, Sakon Dan-jummai ga Matasan Kwasangwami

A nasa bangaren, Mai rikon mukamin shugaban sashen labarai da al’amuran yau da kullum na Pyramid Radio Kwamared Ibrahim Yaro Dawakin Tofa ya roki zababbun shugabanni da kuma wadanda ba suyi nasara ba dasu hada Kansu domin cigaban sashen.

Dawakin Tofa ya ce kowanne nasa ne, inda ya Bada tabbacin yin aiki da kowa domin samun nasarar da aka Sanya a gaba.

Malam Shua’ibu Sani Bagwai shine shugaban kwamitin Zaben, kuma Jim kadan bayan rantsuwar ya bayyana farin cikin sa dangane da hadin Kai da aka basu Wanda ya sa aka gudanar da zaben cikin nasara da kwanciyar Hankali.

A jawabinsa shugaban kungiyar ‘Yan Jaridu na Kasa reshen jihar Kano Kwamared Abbas Ibrahim bayan ya Rantsar da sabbin shugabanni ya bukaci ‘ya’yan kungiyar da su kasance masu hadin Kai cigaban kungiyar.

Ku Karanta: Za Mu Mayar da Hankalin Bunkasa Fannoni Shida Don Gina Sabuwar Kano — Tanko Yakasai

Abbas Ibrahim wanda kuma shine Mai Sanya idanu a zaben ya shawarci ‘ya’yan kungiyar da su kasance masu yafiya da manta dukkan abubuwan da suka faru, yana Mai cewa matukar baa sami hadin Kai ba cigaban da ake nema bazai samu ba.

Ya kuma tabbatar da cewa uwar kungiyar da jihar Kano zata yi aiki kafada-da-kafada domin tallafawa Pyramid Radio.

An dai zabi Aminu Abba Kwaru a Matsayin Shugaba da Yakubu Abubakar Gwagwarwa matemakin Shugaba da Muktar Yahaya Shehu Sakatare da Muhammad Adamu Abubakar Maajiyi da Zakariyya Adam Jigirya Mai binciken Kudi da kuma Adamu Dabo sakataren Kudi.

A zaben dai an kada kuri’u 31 daga cikin mutane 37 da suka cancanci kada kuri’ar inda Aminu Kwaru ya yi nasara da kuri’u 17 yayin da abokin takararsa Abdullahi Muhammad ya sami kuri’u 14, Shima Yakubu Abubakar Gwagwarwa ya sami kuri’u 17 da ya doke abokin takararsa Shehu Suleiman Sharfadi da kuri’u 14.

Idan za’a iya tunawa dai ko a zaben da ya gabata kuri’u uku (3) ne suka raba ‘yan takarar biyu da suka shiga zaben.

Leave a Comment