Siyasa

NNPP ta musanta alaka da PDP

Written by Pyramid FM Kano

Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP ta ce ba ta cikin wata tattaunawa ta kawance da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar gabanin babban zaben da za a yi a wannan watan.

Da yake zantawa da manema labarai a Abuja, Shugaban jam’iyyar na kasa Farfesa Rufa’i Alkali ya bayyana cewa jam’iyyar NNPP ta shagaltu da yadda za ta ci zabe ba wai kulla alaka da wata jam’iyya ko dan takara ba.

Farfesa Alkali ya ce, a cikin dukkan ‘yan takarar shugaban kasa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP Sanata Rabi’u Kwankwaso shi ne ya fi kowa cancanta da kuma shirye-shiryen jagorantar kasar nan kan turbar farfadowa da ci gaba.

Sakatariyar kungiyar yakin neman zaben NNPP, Misis Folashade Aliyu ta ce Sanata Kwankwaso ya bi ta kan hanya domin tattaunawa da ‘yan Najeriya kan hanya mafi dacewa ga kasar.

Leave a Comment