Da Dumi-Dumi

Nasarorin Da Muka Cimma a taron yawon shakatawa Na Duniya

Written by Pyramid FM Kano

Daga: SHEHU SULEIMAN SHARFADI

Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na cigaba da bunkasa raya al’adun gargajiya da yawon shakatawa domin ciyar da jihar gaba.

Kwamishiniyar ma’aikatar raya al’adu da yawon shakatawa ta jihar Kano Hajiya Ladidi Ibrahim Garko ce ta jaddada hakan a taron bikin ranar yawon shakatawa ta duniya wanda ya gudana a hukumar kula da yawon shakatawa dake jihar nan.

Kwamishiniyar ta bayyana cewar taron mai taken “Tourism and Green investment” anyi shi ne takamaimai domin wayar da kan al’umma muhimmancin da yawon shakatawa yake a garesu da kuma tasirin da yake dashi a kan al’umma.

Ta kuma bayyana cewar taken taron yazo a daidai lokacin da dumamar yanayi ke addabar kasashen duniya wanda yake haddasa ambaliyar ruwa da fari.

Don haka a kokarinta na cimma ma’anar taken maaikatarta ta hannun
hukumar Gandun Dabbobin Daji na Audu Bako ta dauki aniyar shuka bishiyoyi kala dari daban-daban da aka samosu daga sassa daban daban na kasashen Afrika.

Kazalika, Hajiya Ladidi Ibrahim Garko ta ce yanzu haka ma’aikatar tana kulla alaka da kuma hadin gwuiwa da takwarorinta na kasashen duniya wadanda suka hada da kungiyar kwadago ta duniya, ma’aikatar yawon shakatawa ta tarayya, cibiyar kula da harkokin yawon shakatawa ta kasa, kungiyar harkokin yawon shakatawa ta kasa da kungiyar kula da harkokin tafiye tafiye ta kasa domin bunkasa ayyukan maaikatar.

Shima a nasa jawabin manajan Darakta na hukumar kula da harkokin yawon shakatawa Alhaji Tukur Bala Sagagi ya bayyana cewar wannan Gwamnatin tasu ta Alhaji Abba Kabir Yusuf tayi alkawarin kafa tarihi a ma’aikatar su kuma zai daga darajar hukumar ta yadda zata yi gogayya da takwarorinta na duniya.

Daga nan sai yayi kira ga ma’aikatansu kan su zage damtse wajen gudanar da aikin su kasancewar harkar yawon shakatawa harka ce mai muhimmancin gaske.

Leave a Comment