Yanzu-Yanzu

Nadin Sarauta: Ibrahim Yaro D/Tofa ya zama Talban Alajawa

 

By: MUKHTAR YAHAYA SHEHU.

Sarkin Alajawa a karamar hukumar Bagwai Alhaji Abubakar M Abubakar ya nada shugaban sashin labarai na Gidan Radiyon Tarayya Pyramid FM Ibrahim Yaro Dawakin Tofa a matsayin Talban Alajawa.

Jim kadan da kammala nadin sarautar a fadarsa da ke garin Alajawa a karamar hukumar Bagwai sarkin ya bayyana cewa nadin sarautar ya biyo bayan sahalewar Madakin Bichi Hakimin Karamar Hukumar Bagwai Alhaji Nura Shehu Ahmad bisa la’akari da irin kokarin sa a sha’anin cigaban yankin.

Sarkin na Alajawa ya hori wadanda aka nada da su cigaba da jajircewa wajen hidimtawa al’ummar yankin Alajawa da karamar hukumar Bagwai da ma jihar Kano baki daya.

A zantawar sa da manema labarai jim kadan da kammala nadin Talban Alajawa Alhaji Ibrahim Yaro Dawakin Tofa ya godewa sarkin na Alajawa bisa amincewa da shi cikin wadanda aka yi wa nadin sarautar.

Sauran wadanda aka nada akwai Umaru Magaji a matsayin Magajin Garin Alajawa da Tukur Adamu a matsayin Sarkin Yakin Alajawa da Isma’il Abubakar a matsayin Yariman Alajawa da Kuma Halilu Alhassan a matsayin Makaman Alajawa.

Leave a Comment