Yanzu-Yanzu

NADIN SARAUTA A MASARAUTAR KANO

 

By: MUKHTAR YAHAYA SHEHU

 

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, JP, CNOL, Ya nada sababbin Hakimai guda shida.

Mai Martaba yayin nadin sabbin hakiman ya ce an nadasu Sarautun ne bisa cancantarsu da irin gudunmawar da suke bayarwa a cikin al’umma.

Cikin sanarwa Mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran masarautar Kano Alhaji Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya ce Wadanda aka nada Sarautun sun hadar da Alhaji Abbas Maje Ado Bayero a Matsayin Bauran Kano da Alhaji Kabiru Ado Bayero a Matsayin San Turakin Kano da Alhaji Umar Ado Bayero wanda aka nada shi Yariman Kano.

Sauran sune Alhaji Tijjani Ado Bayero a Matsayin Zannan Kano da Alhaji Auwalu Ado Bayero a Matsayin Sadaukin Kano da Alhaji Ado Ado Bayero a Matsayin Cigarin Kano.

Mai martaba Sarkin Kano ya hore su da su Sanya halayyar magabatansu na yin koyi da kyawawan halaye wadanda suka hadar da Juriya da hakuri da amana da Kuma tausayawa talakawa.

Ya ce su dauki halayyar magabata ta mika dukkan al’amuransu ga Allah tare da yin biyayya ga wadanda suka tarar a cikin tsarin hakimci da kuma yin da’a kamar yadda suka taso sukaga ana yi Kasancewarsu dukkanninsu yan gidan sarautar Kano ne.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya Kuma bukaci hakiman da aka nada su zamo jakadu nagari a duk inda suka samu kansu tareda gudanar da aikinsu da gaskiya da amana tare da Sanya tsoron Allah.

Leave a Comment