Addini Labaran Jiha

Nadin Lamin Sani Kwamishina Abu Ne Da Ya Dace — Samarin Tijjaniyya

Written by Pyramid FM Kano

Dag: Muktar Yahaya Shehu

Kungiyar Samarin Tijjaniyya ta Kasa ta ce nadin Lamin Sani Zawiyya a matsayin kwamishinan kananan hukumomi da Masarautu na Jihar Kano abune daya dace Kuma a dai-dai lokacin da ake bukata.

Hakan na cikin wata sanarwa da kungiyar ta kasa ta fitar Mai dauke dasa hannun babban Sakataren kungiyar Shehu Tasiu Ishaq da kuma Sakataren yada labarai Abubakar Balarabe Kofar Naisa.

Kungiyar ta ce zabin da Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje yayi na bawa lamin sani wannan ma’aikata ya sake tabbatar da cewa gwamnatin Kano tana ajiye kowanne Mai mukami a gurbin da ya dace domin samun daidaito don cigaban Jihar.

Ku karanta: Ganduje Ya tura Sunan Ali Burum-Burum Majalisa don Nada shi Kwamishina

A bisa hakan ne kungiyar ta bukaci Sabon kwamishinan kananan hukumomin Dakta lamin sani Zawiyya ya bawa marada kunya ta hanyar cigaba da jajircewa dayin aiki tukuru kamar yadda ya Saba.

Leave a Comment