Yanzu-Yanzu

Muna taya Abba Kabir murnar lashe zaben gwamnan kano. Sarkin Kano

By: Mukhtar Yahaya Shehu

 

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya taya zabbben Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf Murna bisa nasarar da ya samu ta lashe zaben Gwamnan Kano a zaben da aka gudanar ranar Asabar data gabata 18th ga wannan wata na Maris.

Cikin wata sanarwa daga Sakataren Yada Labarai na Masarautar Kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ta bayyana cewa al’ummar kasar nan sun karbi tsarin mulkin damokaradiyya da matuqar muhimmaci idan aka yi la’akari da yadda suka futo domin jefa kuri’unsu kamar yadda tsarin mulki ya ba su dama.

Sanawar ta kuma godewa malamai da Limamai da sauran Al’umma bisa addu’ar zaman lafiya da suka dunga yi kafin da kuma bayan gudanar da zaben.

Mai martana sarki ya yi nasiha tare da kira ga sabon gwamnan daya hada kai da dukkanin rukunin al’umma wajen tafiyar da gwamnati, domin yin hakan zai taimaka wajen kyautata rayuwar al’umma da kuma kawo cigaban da ake bukata domin bunkasar tattalin arziki ga jihar Kano da kasa baki daya.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi fatan dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano har ma da sauran sassan kasar nan.

ya yi addu’ar fatan kammala wa’adin mulkinsa lafiya domin cigaban jihar kano.

Leave a Comment