Kasuwanci

Muna Rokon Gwamnatin Tarayya ta Tursasa Dillan Mai Sayarwa a Farashin Gwamnati — Masu Kayan Gwari

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Ibrahim Sani Gama

Kungiyar masu sana’ar kayan gwari ta kasa ta yi kira ga Gwamnatin tarayya ta jihar Kano da su sake yin duba akan yadda farashin man fetur ya yi tashin gwauran zabi a fadin kasar nan tare da Tursasa ‘yan kasuwar su rika siyar da man a farashin Gwamnati.

Shugaban kungiyar Alhaji Hamisu Abubakar ne ya yi kiran a lokacin da yake zantawa da manene labarai dangane da yadda ‘ya’yan kungiyar suke shan wahala a fannin harkokin sufuri.

Hamisu Abubakar ya ce ‘ya’yan kungiyar suna fuskantar matsaloli da kalubale da dama da suka dangaci yadda suke safarar kayan gwari zuwa kudancin Najeriya da sauran jihohin Arewacin kasar nan, musamman ta fannin biyan kudin mota da yiwa kayan su hidima.

Ku Karanta: Bamu Ji Dadin Tsarin Takaita Cire Kudin Da CBN Ya Kawo Ba — Kungiyar Masu Safarar Dabbobin

Ya ce hakan ya faru ne sakamakon tsadar man fetur da kuma yadda yake wahalar samu ga direbobin motoci musamman iskar Gas wanda shine ya fi kowanne tsada, inda ya ce ba wai fannin harkokin kasuwancin kayan gwari kawai matsalar ta shafa ba, ta taba kowanne bangare na rayuwar alummar Najeriya.

Shugaban ya ce akwai bukatar sarakuna da shugabanni masu rike da masarautun gargajiya da malamai da sauran masu ruwa da tsaki a fannoni daban daban su baiwa Gwamnati shawarwarin kawo sauyi a wannan yanayi da alumma suke ciki na matsin rayuwa.

Hamisu Abubakar ya ce ‘ya’yan kungiyar suna taka rawar gani wajen ragewa Gwamnati nauye-nauye da dama da suka hadar da samar da kudaden haraji da samarwa matasa ayyukan yi da bunkasar tattalin Arzikin kasar nan.

Ku Karanta: Kamfanin Galaxy Backbone na bajekolin ayyukansa A babban taron cibiyar sadarwa ta Kasa

Shugaban kungiyar ya kara da cewa suna baiwa Gwamnati cikakken goyan baya a koda yaushe, a don haka ya kamata Gwamnati ta duba halin da suke ciki da sauran masu kasuwanci a fadin kasar nan.

Haka zalika, ya ce duk da cewa sun samu karin kudaden mota wajen safarar kayan su, amma ba su kara kudaden kayan gwarin da suke kaiwa ba, inda ya ce koda hakan ma ya kamata Gwamnati ta tallafawa ‘ya’yan kungiya da sauran alummar Najeriya baki daya.

Daga bisani ya bukaci ‘ya’ya da su kasance masu bin dokokin da kungiya da hukumomi da suke da alhakin kulawa da al’amuran kasuwanci suka zartar musamman Gwamnati domin kaucewa karya dokokin da aka sanya.

Leave a Comment