Labaran Jiha

Muna Rokon Gwamnatin Kano ta Gyara Titin Railway zuwa Audu Bako — Mamuda Zango-Kabo

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Ibrahim Sani Gama

Kungiyar Matasa ta kasuwar masu magunguna ta yi kira ga Gwamnatin jihar Kano da hukumar dake kula da gyaran KARMA da su gyaran Titin da ya tashi daga Railway zuwa shataletalen gidan Mai A A Rano zuwa titin Audu Bako way.

Shugaban kungiyar kuma, mai rajin ci gaban alummar a jihar Kano, Alhaji Mamuda Zangon Kabo ne yayi wannan kiran la’akari da yadda alumma suke fuskantar wahala a lokacin amfani da Titunan.

Ya ce, kamata yayi Wanda alhakin gyaran ya rataya akansu suyi duba na tsanaki domin sanin gyaran da za”a yiwa hanyoyin domin lalacewar ta yi mutukar ta’azzara.

Ya ce, rashin magudanan Ruwa yana da ya Daga cikin abubuwan da yake haifar da yawan ambaliyar Ruwa a yankunan da dama a fadin jihar, inda ya bukaci alumma da su kasance suna aikin gayya da share magudanan Ruwa domin kaucewa yawan ambaliyar Ruwa da ta yi yawa a halin yanzu.

Ku karanta: Zamu Goyi Bayan Duk Jam’iyar Da Zata Karbo Hakkin Yan Kungiyar Mu da Aka kashe — Mustapha Ali

Haka zalika, ya yabawa Gwamnatin jihar Kano, bisa kafa kwamatin da zai rika lura da gyaran magudanan Ruwa da guraren da suka yi gine gine ba bisa kaidaba musamman a hanyoyin Ruwa, Wanda yin haka na Daga cikin abubuwan dake haifar da Ambaliyar Ruwa da zubewar gine gine a lokuta daban-daban.

Ya shawarci masu hannu da shuni da su ci gaba da tallafawa Matasa a unguwanni domin share magudanan Ruwa da yin ayyukan gayya don zai taimaka kwarai kaucewa yawan ambaliyar Ruwa.

Leave a Comment