Kasuwanci

Muna Rokon CBN Ya Kara Lokacin Karbar Tsohon Kudi — Aminu Mai-kurkura

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi

Kungiyoyin yan kasuwa na cigaba da kiraye kirayen babban bankin Nigeria CBN da ya kara wa’adin da ya sanya na 31 ga watan janairun 2023 domin daina karbar tsofaffun kudade.

Shugaban matasan yan kasuwar singa Alhaji Aminu Mai-kurkura wanda lawan Dan Hajiya mai rice ya wakilta ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa.

Lawan Dan Hajiya ya ce yan kasuwa na cikin kalubale dangane da wannan Wa’adin da gwamnati da CBN suka sanya na dakatar da karbar tsofaffin kudade wajen gudanar da hada hadar kasuwacinsu na yau da kullum.

Ya bukaci gwamnatin ta sake yin duba na tsanaki domin kara lokaci musamman saboda alummar karkara da suke shigowa cikin garin domin siyayyar kayayyakin da suke kasuwacinsu.

Ku Karanta: Muna Bukatar Tallafin Gwamnatoci Don Bukasa Kasuwancin mu — Shugaban Kasuwar Gyada

Ya kuma jaddada cewar yanzu haka wadansu guraren sun dakatar da karbar tsoffin kudade domin kaucewa gudun tafka asara, amma akwai bukatar yin duba na tsanaki a kan kananan yankasuwa da suke bukatar su samu damar shigar da kudadensu.

A jawabinsa Sakataren kungiyar kasuwar Singa dake gidan Abdurrashid Mai-turare Alhaji Auwalu Ahmed rijiyar lemo yace da yawa wasu bankunan idan kaje babu sabbin kudaden wanda kamata yayi kudaden su wadata a bankunan wannan shi zai sanya a samu yawaitar sabbin kudaden a hannun alumma musamman yan kasuwa.

Ku Karanta: Mun Shirya Ceto Kano, Inganta Kasuwanci Da Gina Al’umma Idan Mukayi Nasarar Cin Zabe — Tanko Yakasai

Kazalika Auwalu rijiyar lemo ya shawarci yan kasuwa musamman kanana dasu rika baiwa masu sanaar P. O. S domin tura musu kudadensu zuwa asusunsu da zarar sun kammala kasuwacinsu a ranar, har zuwa nan da lokacin da gwamnati ta sanya waadin dakatar da karbar tsoffin kudaden.

Leave a Comment