Ilimi

Muna Kara Jaddada Baiwa Gwamnatin Goyan Baya Domin Ciyar Da Ilimi Gaba

Written by Pyramid FM Kano

Daga: IBRAHIM SANI GAMA

Kungiyar masu sana’ar siyar da littafai ta jihar Kano reshen kasuwar Sabon Gari ta bukaci Gwamnatin jihar mKano data yi duk mai yiyuwa wajen ganin ta dakile matsalar da iyayen yara suke fuskanta wajen neman littatafan karatun ‘ya’yansu a kasuwannin jihar.

Jami’in Hulda da jama’a na kungiyar Alh. Umar Musa Gama ne ya bayyana haka a lokacin da wasu iyayen yara suke kokawa yayin da suka zo siyan littafai a kasuwar Sabon Gari dake nan jihar Kano.

Yace, kungiyar ta dade tana karbar irin wadan nan korafe-korafen akan wannan lamari amma hakarta bata cimma ruwa ba, saboda haka yanzu lokaci yayi da ya kamata iyayen yara su baiwa Kungiyar cikakken hadin kan da suka kamata wajen ganin an kawo karshen matsalar dake faruwa a fannin harkokin ilimi a jihar Kano.

Haka zalika, ya bayyana cewa, kungiyar za ta yi iya koarinta domin ganin ta samu Shugaban Majalisar Dokoki na jihar kano, kasancewar sun taba zuwa wajen Shugaban majalisar a wancen lokaci domin yiwa wannan tsarin doka, amma basu samu nasara ba, yanzun ma za su sake gwadawa domin ganin an yi masa doka a majalisar.

Yace, amma hakan ba zai samu ba, har sai iyayen yara sun basu goyan baya da hadin kai yadda ya kamata kafin samun wannan bukata da suke da ita na kawo karshen matsalar dake faruwa a bangaren ilimi.

Umar Musa Gama yace, akwai wata mata da ta zo domin siyawa ‘ya’yanta littattafai, amma sakamakon kudaden yayi yawa suka rage mata amma duk da haka sai ta shiga cikin kudaden abincinsu, aanda wadannan yaran su hudu duka marayune.

Umar ya shawarci iyayen yara, da su yi kokari wajen zama da kungiyar iyayen yara ta makarantu domin neman hadin kan ta na kawar da wannan kalubale da ya ki ci, ya ki cinyewa makarantu masu zaman kansu dake fadin jihar Kano.

Leave a Comment