Ilimi

Muna Bukatar Tallafin Iyaye, Dattawa da Gwamnatin Don Gina Matsuguni na Din-Din-Din — Shugaban B. I. T.

Written by Pyramid FM Kano

Shugaban Makarantar koyar da harkokin Kwamfiyuta da yada labarai wato “Bootstrapping Information Technology (B.I.T)” ya bukaci iyayen Yara da Masu ruwa da tsaki harma da gwamnatoci da su tallafawa makarantar domin gina Matsuguni na din-din-din domin cigaban harkokin koyo da koyarwa.

Ahmad Umar Abdurazak ya bayyana hakan ne lokaci bikin yaye daliban makarantar su dari uku da hamsin (350) wanda ya gudana a Unguwar hotoron Kudu dake yankin karamar hukumar Nassarawa a Kano.

Ya ce B. I. T. tana da rassa bakwai a cikin kwaryar birnin Kano sai Kuma rassa guda biyu, daya a jihar Jigawa da a jihar Katsina, kuma daliban makarantar suna samun horo a na Kwamfiyuta da Harkokin yada labarai da kanann sana’o’i da sauran su.

Shugaban ya ce makarantar bata da Matsuguni na din-din-din a reshen ta dake Hotoro sai dai tana amfani da makarantun Gwamnatin domin gudanar da harkokin koyo da koyarwa dukka a kishin ta na koyawa Yara amfani da Kwamfiyuta da kuma Internet domin cigaban harkokin ilimi da kasuwanci da kuma zamantakewar al’umma.

Ku karanta: SAS Ta Bada Gagarumar Gudun Mowa a Rayuwar Mu — Abdullahi Maikano

Daga nan ya bukaci iyayen Yara da su mayar da hankali wajen bibiyar karatun ‘ya’yan su da kuma tallafawa makarantar da yayan ke karatu a ciki.

A jawabinsa, dagacin hotoron Kudu a Karamar hukumar Nassarawa Alhaji Ashiru Abubakar ya ja kunnen dalibai da mayar da hankali wajen bibiyar karatun da ake musu, sannan su guji yi amfani da internet ko wayoyi ta hanyar da bata dace ba kamar su bata lokaci a “social media” ko kallo ko yada labarai ko hotuna ko Kuma hotuna masu motsi wadanda basu dace ba.

Dangane da rokon makarantar na bude mata wata cibiyar Kwamfiyuta kuwa, Alhaji Ashiru Abubakar Yusuf ya ce zai tattauna da masu ruwa da tsaki dake lura na cibiyar domin basu damar amfani da ita matukar hakan bazai kawo nakasu a cibiyar ba.

Dagacin ya kuma yi fatan Iyaye zasu cigaba da jajircewa wajen bibiyar karatun ‘ya’yan su da daukar matakan da suka kamata da nufin kula da tarbiyar ‘ya’yan su, yana mai cewa ta haka ne za’a samu al’umma ta gari.

A nasa bangaren, daya daga cikin iyayen makarantar, kuma shugaban kungiyar direbobin Motar Dakon Mai Tai kasa reshen jihohin Kano da Jigawa da Katsina da kuma Yobe Muhammad Sani Malam ya ce tallafawa harkokin ilimi nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa, saboda haka ya yi kira ga sauran shugabanni da masu ruwa da tsaki da su rika tallafawa fannin ilimi tun daga tushe don samun al’umma ta gari.

Ku karanta: Za Mu Yi Amfani Da Duk Abin Da Ke Hannun Mu Domin Cigaban Kwalejin CAS — Ali Saadu Birnin-kudu

Ya ce Nauyi yayi wa gwamnatoci yawa, kuma matukar ana son cigaban harkokin ilimi dole “me taro Mai Siri, iyayen Yara masu hanu da shuni su tallafa.

Muhammad Sani Malam yayi alkawarin cigaba da tallafawa harkokin ilimi a nan jihar Kano da ma kasa baki da nufin cigaban al’umma.

Leave a Comment