Tattalin Arziki

Muna Bukatar Tallafin Gwamnatoci Don Bukasa Kasuwancin mu — Shugaban Kasuwar Gyada

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Ibrahim Sani Gama

Kungiyar yan kasuwar gyada dake jihar kano sun koka dangane da rashin tallafi daga Gwamnatin jiha da ta tarayya bisa tallafawa ‘ya’yanta ta hanyar basu jari da zamanantar da harkokin kasuwancin su.

Shugaban matasa na kungiyar Alhaji Aminu inuwa ne ya bayyana haka ga manema labarai a ofishinsa dake Tafawa balewa a karamar hukumar Nassarawa dake nan Kano.

Aminu inuwa ya ce akwai tallafi kala-kala da Gwamnatoci suka baiwa wasu kungiyoyin a Kano, amma kungiyar yan kasuwar gyada basu taba samu ba, duk gudunmawa da goyan baya da kungiyar take baiwa Gwamnatoci.

Ku Karanta: Matasa Ku Guji Shiga Ayyukan Bata Gari — Kwamared Rabi’u Tumfafi

Shugaban ya ce jihar Kano cibiyace ta kasuwancinsu da yakamata Gwamnati ta bijiro da abubuwan da za ta taimakawa matasa su kaucewa zaman kashe wando da shiga ayyukan batagari da sauransu.

Ya kara da cewa harkokin kasuwancinsu ana mutukar bukatar su a koina a Duniya kasancewar sana’a ce da take bukatar Gwamnatoci, musamman ta jihar kano su kawo hanyoyin da za su bunkasata da zamanantar da ita don yin gogayya da sauran kasashen Duniya.

Ku Karanta: Mun Shirya Ceto Kano, Inganta Kasuwanci Da Gina Al’umma Idan Mukayi Nasarar Cin Zabe — Tanko Yakasai

Ya ce idon aka yi duba da lokutan da suka gabata akwai sauye sauye da aka samu na farashin kayayyaki da karyewar tattalin arziki a jihar kano abune dake bukatar Gwamnatoci su shigo damin zamanantar da harkokin kasuwancinsu da kuma basu tallafi kamar sauran kungiyoyin yan kasuwa.

Haka zalika, yayi kira ga matasa da su kasance masu biyayya da dogaro da kawunansu, da kuma ci gaba da baiwa shugabancin kungiyar hadin kai domin samun bijiro da managartan abubuwan ci gaba da nufin inganta harkokin kasuwancinsu.

Leave a Comment