Kasuwanci

Muna Bukatar Tallafin Gwamnatin Kano Inji Kungiyar Masu Kayar Gwari

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Ibrahim Sani Gama

Kungiyar masu sana’ar kayan gwari ta jihar Kano ta bukaci Gwamnatin tarayya da ta jihar Kano da su kawowa fannin harkokin noma daukin gaggawa domin farfado da fannin.

Shugaban kungiyar Malam Hamisu Abubakar ne ya bukaci hakan duba da sauye_sauye da ake samu a fannin harkokin Amfanin gona a wannan lokacin da ya kamata a ce ana samun saukin kayayyaki.

Hamisu Abubakar ya ce akwai bukatar gwamnati ta kawo wasu sabbin tsare-tsaren da za su agazawa manoma da masu sana’ar kayan gwari ta fannoni tallafawa Yan kasuwa da za su inganta rayuwar ‘ya’yanta da sauran alummar gari, inda ya ce idon suka samu sauyi da sauki su basa wani yunkurin gallazawa mutane musamman ta bangaren kasuwancinsu na yau da kullum.

Ya ce dukkannin tallafawa da Gwamnatoci suke cewa sun yi a fannonin yan kasuwa daban-daban a kasa ko a jiha bai taba samun kungiyar masu sana’ar kayan gwari ba.

Ku Karanta: Muna Bukatar Tallafin Iyaye, Dattawa da Gwamnatin Don Gina Matsuguni na Din-Din-Din — Shugaban B. I. T.

Shugaban kungiyar ya kara da cewa, kungiyoyi daban daban sun fito da yawa da nufin cewa daga gwamnati suke akan gwamnati za ta ba da tallafi amma shiru kake ji shi yasa yake kira ga Gwamnatoci a matakai daban daban, idon za ta ba da wani tallafi, to ta nemi shugabancin kungiya domin tattaunawa da shi.

Ya ce idon Gwamnati tana yin haka ba za a rika samun korafe-korafe ba daga kungiyoyi ko kuma daidaikun jama’a ba wajen ba da tallafi da taimako daga Gwamnatoci ko yan siyasa ba.

Shugaban ya yabawa Gwamnatin jihar Kano, bisa kokarinta na ganin ta inganta rayuwar alumma da kawo managartan shiye shirye domin ciyar da Kano gaba musamman ta fannin harkokin yaki da shan miyagun kwayoyi inda ya ce kungiyar masu sana’ar kayan gwari dake karkashin gadar masallacin Fagge da kasuwar kofar wambai ta himmatu wajen dakile masu ta’ammali da miyagun kwayoyi ko batagarin alumma dake cikinsu har ma Dana waje da za su je domin su fake a cikin su.

Ku Karanta: Ku Kyauta Rayuwar Al’umma Da Kudaden Shigar Ku, Aminu Ado Ga Gwamnatoci

Hamisu Abubakar ya ce, kungiyar ta dade tana tattarawa Gwamnatin jiha da tarayya kudaden haraji amma har yanzu ba’a kai mata wani dauki na taimako daga Gwamnati ba, yana Mai cewa har yanzu suna sanya ido domin ganin wanda zai baiwa kungiyar tallafi ba.

Shugaban ya kuma yi kira ga ‘ya’yan kungiyar da su ci gaba da baiwa shugabancin kungiyar cikakken goyan baya da hadin kan daya dace domin samun bijiro da managartan tsare tsare da za su bunkasa kasuwancinsu.

Leave a Comment