Labaran Jiha

Muna Bin Gwamnatin Kano Kusan Miliyan Dubu 37 a Watanni 4 — Yan Fansho

Written by Pyramid FM Kano

Kungiyar yar Fansho ta kasa Kasa reshen jihar Kano ta ce tana bin Gwamnatin jihar Kano Kusan Naira Miliyan Dubu 37 a cikin Watanni hudu na hakkin maaikatan da sukayi ritaya baa biya su hakkin su ba.

Kungiyar karkashin jagorancin kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Kano NLC ta bayyana hakan a wata zanga-zanga da ta gudanar wacce shugaban NLC na Kano Kwamaree Kabiru Ado Munjibir ya jagoranta.

Ya ce Daga Watan Yunin shekarar 2022 zuwa Watan Satumbar 2022, ‘ya’yan kungiyar sun bin Gwamnatin jihar Kano naira Miliyan Dubu 36 da miliyan 900 wanda ya shafi ‘yan Fansho su dubu 18 da 971 da ba’a biya su ba.

Ya ce daga shekarar 2006 zuwa 2022, ‘yan Fansho suna bin Gwamnatin jihar Kano miliyan Dubu 69 da Miliyan 200 wanda wasu hukumomi da maaikatun Gwamnatin basu kaiwa hukumomin da abin ya shafa domin biyan ‘yan Fansho hakkin su ba.

Kabiru Minjibir a madadin ‘yan Fansho sun bayyana takaicin su yadda wasu hukumomi da maaikatun Gwamnatin a nan Kano basa Mika kason kudin da ya kamata su rika mikawa ga hukumar kula da harkokin Fansho ta jihar Kano domin bayan ‘yan Fansho hakkin su.

Kabiru Ado Munjibir ya ce hukumomin da basa bayar da kason su, sun hada da ma’aikatar kanann hukumomi da masarautu da hukumar kula da ilimin Bai daya ta jihar Kano SUBEB da sauran su.

Ku karanta: Za Mu Yi Amfani Da Duk Abin Da Ke Hannun Mu Domin Cigaban Kwalejin CAS — Ali Saadu Birnin-kudu

‘Ya’yan kungiyar sun Kuma koka kan yadda ake Yanke musu wani kaso na kudaden fashon su a duk wata, inda suka roki Gwamnatin da ta dakatar da yanke musu kudaden.

A jawabinsa, gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje Wanda shugaban ma’aikata na jiha Usman Bala ya wakilta ya basu tabbacin Gwamnatin jihar Kano na biyan dukkan kudaden fasho a duk wata.

Ya ce matsalar da aka samu shine yadda adadin kudaden da ake cira daga ma’aikata basa kaiwa adadin kudin da ake bukata wajen hadawa domin biyan ‘yan Fansho a nan Kano, amma duk da haka Gwamnatin jihar Kano tana iya kokarin ta ba biyan ‘yan Fansho hakkokin su a duk wata a nan Kano akasin yadda wasu jihohin kasar nan ake binsu kudin Fansho na tsawon lokaci.

Usman Bala daga nan ya ce dukkan korafe-korafen sun za’a Mika su ga gwamna domin daukar matakan da suka da ce.

Leave a Comment