Siyasa

Mun Shirya Ceto Kano, Inganta Kasuwanci Da Gina Al’umma Idan Mukayi Nasarar Cin Zabe — Tanko Yakasai

Written by Pyramid FM Kano

Dan Takarar gwmnan jihar Kano a karkashin tutar Jam’iyar PRP Salihu Tanko Yakasai ya ce shi da Jam’iyar sa sun shirya tsaf domin ceto jihar Kano daga halin da ta sami kanta a cikin na rashin iya shugabanci tare da ingata rayuwar al’umma matukar yayi nasara a zaben dake tafe.

Salihu Tanko Yakasai ya a bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci gidan Radio Tarayya Pyramid FM dake Lamba Uku kan titin Audu Bako a cikin birnin Kano.

Ya ce yana ziyarar ne domin hada hanu da kafafen yada labarai musamman na Radio la’akari da muhimmancin da suke dashi wajen aika sako cikin al’umma musamman a arewacin Nigeria.

Ku Karanta: Zaben 2023: Ku Zabi Shugabanni Na Gari Kamar Gawuna — Tanko Yakasai

Tanko Yakasai ya yi fatana zaiyi aiki kafada da kafada da Pyramid Radio idan yayi nasara domin yin aiki tare wajen daga darajar al’umma jihar Kano da inganta kasuwancin al’ummar jihar.

A cewarsa, “Nine Dan takarar gwamna na Farko a tarihin jihar Kano da ya fara kaddamar da manufofin sa wanda indan yayi nasara zai mayar da hankali a kansu, yana mai cewa duk mai so ganin manufofin yana iya ziyartar shafin intanet na www.dawisu.com domin karantawa”.

“Nasan muhimmancin da radio take das hi musamman a arewa saboda nayi aikin jarida sama da shekaru 6 a gidan radio Freedom, insha Allah za mu yi aiki tare domin cigaban alumma, muna neman goyon bayan ku don samun nasara”, inji shi.

Ya ce jam’iyar PRP ta na da tarihi a jihar Kano dama arewacin Nigeria la’akari su Malam Aminu Kano da suka kafa ta da irin gudun mowar da suka bayar a cigaban Kano inda ya roki al’ummar jihar Kano da su Zabi jam’iyar PRP domin farfado da Kano tare da kaita tudun mun tsira.

Ku Karanta: Za Mu Mayar da Hankalin Bunkasa Fannoni Shida Don Gina Sabuwar Kano — Tanko Yakasai

Ya ce mafi yawan Yan takarar Matasa ne masu jini a jika wanda matukar al’ummar jihar Kano suka zabe su, zasu Bada gudun mowa domin samarwa da matasa Yan uwansu aikin yi da aiwatar da tsare-tsaren inganta rayuwar mata da kanana yara da ma cigaban kowa da kowa.

A jawabinsa, shugaban gidan Radio Tarayya Pyramid FM Malam Abba Bashir ya bayyana cewa gidan Ako da yaushe a shirye yake yayi aiki da dukkan masu ruwa da tsaki domin cigaban tattalin arzikin mutanen Kano dama Nigeria ba ki daya.

Abba Bashir ya ce abin farin cikin ne kan yadda Salihu Tanko ya kafa tarihi a matsayin Dan takarar gwamna na Farko da ya ziyarci pyramid radio domin Neman goyon bayan ta da nufin cigaban al’umma.

Ya ce gidan a karkashin jagorancin sa zai gudanar da ayyukan sa bisa doron Doka tare da tallafawa Dantakarar domin samun nasara.

Ya kuma ce a shirye yake yayi aiki da duk wata jam’iyar siyasa wacce keda burin ganin cigaban al’umma da tattalin arzikin Kano da kuma ganin an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.

Leave a Comment