Da Dumi-Dumi Labaran Jiha

Mun Sami Nasarar Cafke Jabun Magani Na Feye Da Miliyan 50 – Karota

Written by Pyramid FM Kano

Daga: KABIR GETSO

Hukumar kula da Tituna da ababen hawa wato Karota ta sami nasarar cafke jabun magunguna a kan titin Murtala Mohammed da ke birnin Kano.

Lokacin da direban motar yake ƙoƙarin shiga kasuwar Sabon Gari domin rabawa a cikin shaguna.

Daga cikin magungunan da aka cafke sun hada da: Maganin ciwon jiki, maganin zazzaɓi, maganin Tari, da sauran su.

Shugaban Hukumar KAROTA Engr. Faisal Mahmud Kabir yace Hukumar KAROTA baza ta zuba ido ta bari ana ta’ammuli da miyagun kwayoyi a jihar Kano ba.

Shugaban hukumar ya kara jan hankalin al’umma da su guji siyan magani a wajen da bai karanta ba domin gujewa fadawa cikin matsala.

Yace ƙofar Hukumar a buɗe take wajen karɓar bayanin sirri domin daƙile yawaitar jabun magani a faɗin jihar nan baki daya.

Leave a Comment