Kasuwanci Tattalin Arziki

Mun Horar Da Matasa 350 Gyaran Waya A Shekara Daya — Shugaban “Huzy Comms”

Written by Pyramid FM Kano

Cibiyar “Huzy Communication & Associates” ta ce ta Horar da Matasa Maza da Mata 350 yadda ake gyaran wayoyin hanu kala-kala domin dogaro da Kai.

Shugaban cibiyar Huzaifa Ahmad Muhammad ne ya bayyana a bikin yaye daliban wanda suka kasance mata a kasuwar gyaran wayoyin hanu ta Beirut dake yankin karamar hukumar Fagge a nan Kano.

Ya ce matasan da aka yaye an tabbatar kowanne daga cikin su ya iya gyaran kowacce waya aka kai masa, sannan kuma an koya musu dabarun ayyukan su a cikin sauki.

“Mun fara a ranar 1 ga watan Janairun 2022 ta bana, kuma mun fara da daliban da basu wuce 15, amma a yanzu muna yaye dalibai 350 wanda suka samu horo daban-daban da suka kasance mata da maza”, inji Huzaifa.

Ku Karanta: 2023: Za Tabbatar An Zabi Shugabanni na Gari — Gidauniyar Ibrahim Khalil

Huzaifa Muhammad ya kuma bayyana farin cikin sa ga Allah Madaukakin sarkin, inda kuma yayi fatan alkhairi ga wadanda suka halarci taron tare da fatan zasu koma gida lafiya.

A jawabinsa, mataimakin Gwamnan jihar Kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya ce gwamnatin jihar Kano ta ce zata tallafawa cibiyar horar da matasan domin samawa matasa aikin.

Gawuna wanda maitamaka masa na musamman a ayyukan na musamman Abubakar Garba Indabawa ya wakilta ya ce gwamnatin zata duba yuwuwar samawa matasa kayayyakin da zasu rika gudanar da sana’o’in su wanda hakan zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin jihar Kano.

Ya ce gwamnatin jihar Kano da dauki Nauyin kwararru daga kasashen ketare wanda suke zaune a nan Kano, suke kuma koyawa mutanen Kano sana’o’in dogaro da kai, don haka Gwamnati zata tallafawa matasan da aka yaye ta fuskoki da dama da nufin dorewar sana’o’in da suka koya.

Ya ce koyar da sana’o’in dogaro da Kai yana daga kudirin Gwamnatin jihar Kano, a don haka zata cigaba da yin duk mai yuwuwa domin samun nasara.

A sakon da ya aike da shi, Sakataren Gwamnatin jihar Kano Alhaji Usman Alhaji wanda mai taimaka masa na musamman a harkokin ICT ya wakilta ya bada tabbacin ofishin sakataren gwamnatin na ganin ya tallafawa kungiyoyi da kamfanin a harkokin sadarwa da nufin cigaban alummar jihar Kano.

Ku Karanta: Zamu Wayar Da Kan Mutane Game Da Ayyukan Raya Kasa na Ganduje — Bashir Rufa’i

Usman Alhaji ya buma ce kofarsa a bude take a Koda yaushe domin tallafawa kowanne yunkuri na cigaban matasa.

Da yake karbar Lambar girmamawa da aka bashi, Tafidan Kano Hakimin Fagge Dakta Mahmud Ado Bayero ya bukaci masu ruwa da tsaki da su tallafawa “Huzy Communication & Associates” domin cigaban matasan da suke koyon sana’o’i a ciki.

Mahmud Ado Bayero ya kuma jaddada kudirin majalisar masarautar Kano na tallafawa dukkan matakan da suka dace domin cigaban matasa, wanda a cewarsa matasa suke kashin bayan cigaban kowacce al’umma.

Tafidan na Kano daga nan ya bukaci sauran shugabanni da su tallafawa cibiyar domin samun nasarar da aka sanya a gaba.

Taron ya samun halartar shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano Haroon Muhammad Ibn-sina wanda yayi alkawarin bawa biyu daga cikin wadanda aka yaye aiki a hukumar Hisbah da tsohon shugaban gidan bunkasa harkokin dimukuradiyya da cigaba dake gidan Mumbayya Farfesa Habu Muhammad Fagge da sauran wasu da dama.

Leave a Comment