Yanzu-Yanzu

Mun Gamsu da yanayin aikin Titin Kano zuwa Abuja -Fashola

By: KABIR GETSO

 

Minstan Ayyuka da Gidaje Babatunde Raji Fashola ya bayyanna gamsuwarsa dangane da yadda aikin titin Kano zuwa Abuja ke gudana a halin yanzu.

Fashola ya bayyanna hakan ne a ziyarar aikin da ya kawo wanda ya sauka a nan Kano tare da rakiyar Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Kwamishinan Ayyuka da Gidaje na jihar Kano Alh. Sunusi Wada Saleh, inda tawagar ta fara sauka a yadin farko dake garin Dakatsalle a karamar Hukumar Garun Malam.

Da yake jawabi Ministan yace, aikin titin kashi uku ne, akwai kashi na farko wanda ya tashi daga Kano zuwa Zariya, sai kashi na biyu wanda ya tashi daga Zariya zuwa Kaduna, sannan sai kashi na uku wanda shi kuma ya tashi daga Kaduna zuwa Abuja.

Ya kara da cewar aikin Titin Zariya zuwa Kaduna zai kammalu zuwa karshen makon nan yayinda aikin Kano zuwa Zariya shima zai kammalu daga nan zuwa karshen wa’adin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ko da aka tambayi batun aikin wanda ya tashi daga Kaduna zuwa Abuja halin da ake Ciki? Sai Shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban kasa farfesa Ibrahim Gambari wanda shima yana cikin tawagar yace, aikin ba abune da za’a iya cewa komai ba kai tsaye sai anyi la’akari da wasu muhimman abubuwa. Amma aikin ana nan anayin sa yadda ya kamata kuma Gwamnati zatayi iya kokarinta don ganin aikin ya kammalu cikin nasara.

Leave a Comment