Kasuwanci

Mun Gamsu Da Tsarin CBN Na Takaita Kudade A Hanun Mutane — Rabi’u Tumfafi

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Ibrahim Sani Gama

Kungiyar kasuwar Abinci ta Dawanau dake karamar hukumar Dawakin Tofa, ta bayyana gamsuwarta da tsarin da Babban Bakin Najeriya (CBN) ya bijiro da shi na takaita zirga zirgar kudade a hannun alummar kasar nan.

Sakataren kungiyar kuma Garkuwar matasan Arewacin Najeriya, Kwamared Rabiu Abubakar Tumfafi ne, ya sanar da haka a lokacin da yake zantawa manema labarai a jihar Kano dake Arewacin Nigeria.

Rabi’u Tumfafi ya ce takaita zirga-zirgar kudaden a hannun alumma za ta ragu saboda tsari da CBN ya fito da shi zai taimakawa yan kasuwa wajen aiwatar da kasuwancinsu na yau da kullum.

Ku Karanta: Bamu Ji Dadin Tsarin Takaita Cire Kudin Da CBN Ya Kawo Ba — Kungiyar Masu Safarar Dabbobin

Garkuwar matasan ya kara da cewa ta fannin yawo da makudan kudade da wasu daga cikin alumma suke yi ko da yaushe zai zama tarihi duba da hada hadar kasuwancin da suke yi, musamman masu zuwa wasu jihohin Najeriya domin siyo kayayyaki domin a cewarsa hakan zai taimaka wajen kaucewa barayi da sauran wata fargaba da suke tunanin za ta iya afkuwa akan hanyoyin da suke zuwa fatauci.

Sakataren ya ja hankalin matasan Arewacin Najeriya da su kaucewa shiga cikin bangar siyasa, musamman sakamakon yadda lokacin babban zabe yake karatowa wanda ya jaddada cewa, kamata yayi matasan su yi amfani da wannan dama wajen zaben shugabanni nagari da za su taimakawa rayuwarsu da alummar kasar nan, musamman Daliban da suka kammala karatu basu samu ayyukan yi ba da bijiro da managartan tsare tsaren inganta rayuwa da farfado da tattalin arzikin kasa, kasacewar Najeriya ta samu kanta a wani yanayi da yake bukatar matasa su kawo dauki domin sune shugabannin gobe.

Garkuwar ya Kara da cewa, kasancewarsa garkuwar matasan Arewacin Najeriya, ya ga dacewar amfani da wannan dama wajen wayarwa matasa kawunansu da basu shawarwari da za su Nesanta Kansu da shiga cikin bangar siyasa duba da halin da alummar kasar nan, suka samu Kansu a ciki.

Ku Karanta: Matsalar mu Shine Gwamnatoci Basa Tallafawa Masu Safarar Shanu — Mustapha Ali

Ya ce idan matasa suna bari ana amfani da su wajen cin mutuncin wasu abokanan burmin siyasa ta hanyar basu muggun kwayoyi da makamai da sauran abubuwan da za su iya haifar da tarzoma da hargitsi da rikici tsakanin alumma wanda zai kai ga rasa rayukan alumma.

Daga nan ya yabawa matasan Arewacin Najeriya bisa yadda suka jajirce wajen Neman ilimi saboda da ilimi ne ake samun ci gaba a koina a Duniya.

Leave a Comment