Labaran Jiha

Mun Gamsu Da Shirin Egypt Na Samar Da Kamfanin Shinkafa a Kano — Aminu Ado

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Muktar Yahaya Shehu

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana gamsuwar sa akan aikin da kasar Egypt za ta yi na samar da katafaren kamfanin shinkafa domin bunkasa cigaban samar da Shinkafa a jihar Kano.

Alhaji Aminu Ado Bayero CFR ya bayyana haka ne lokacin da yake karbar bakuncin shugabanin Gwamnatin Kasar Egypt dangane da aikin samar da wani kamfanin samar da shinkafa da zasu kafa a nan jihar Kano.

Cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran masarautar Kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya fitar ta ambato mai Martaba Sarkin yana cewa dangantakar dake tsakanin kasar masar da Nigeria musamman jihar Kano dangantaka ce dake kara habaka tattalin arzkin Kano da kasa baki daya.

Ku Karanta: Za Mu Cigaba Da Bada Gagarumar Gudun Mowa a Bangaren Lafiya — Aminu Ado

Ya ce masarautar Kano za ta bayar da gudunmawar data dace don bunkasar tattalin arziki kasar nan.

Mai Martaba Sarkin ya kuma yabawa kasar ta masar bisa gudummawar da suke bayarwa wajen ilimantar da al’ummar a kasar nan.

A nasa jawabi Shugaban kamafanin Egta Alhaji Bashir Yusif Ibrahim ya ce, jihar Kano zata ci gajiyar samar da kamfanin shinkafa mafi girma a kasar nan wanda kasar masar zata samar.

Ku Karanta: Rejista Da Karbar Katin Dan Kasa Na Da Matukar Muhimmanci — Aminu Ado

Haka zalika a wani cigaban kuma Mai Martaba Sarkin na Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya karbi bakuncin shugabanin hukumar zakka da Hubsi ta jiahr Kano karkashin jagorancin shugaban majalisar limaman juma’a Shekh Muhammad Nasir limamin masallacin shekh Ahmadu Tijjani dake Kofar Mata a nan Kano.

Leave a Comment