Muhalli

Muhalli: Ku Zuba Jari A Mayar Da Shara Dukiyi, Gwamnatin Kano Ga Kamfanonin Gida

Written by Pyramid FM Kano

Gwamnatin jihar Kano ta bukaci kamfanoni na cikin gida da su zuba jari mai yawa wajen sauya shara zuwa kayayyakin amfani tare da yaki da matsalar dumamar yanayi don bunkasa muhalli da nufin cigaban alumma.

Kwamishinan muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bukaci hakan a lokacin da ya jagoranci bude  taron karawa juna sani game da harkokin shara da cigaban muhalli wanda ya guidana a nan Kano.

Cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai da wayar da kan jamaa na maaikatar muhalli ta jihar Kano Ismail Garba Gwammaja ya sanyawa hanu ta ambato kwamishinan na bayyana karfin gwiwarsa wajen yin aiki da dukkan masu ruwa da tsaki da nufin yaki da matsalolin muhalli wanda ya ce taron zai mayar da hankali wajen lalubo matsalolin da hanyoyin da zaa magance su.

Ku Karanta: TSAFTAR MUHALLI: Gwamnatin Kano Ta Bawa Kasuwar ‘Yan-lemo Wa’adin Kwanaki Uku

Ya ce maaiktar muhalli zata bawa duk wani tsari hadin kai da zai bada gudun mowa a yaki da matsalar dumamar yanayi a jihar Kano dama arewacin Nigeria baki daya.

Haka kuma kwamishinan ya yabawa maaikatar muhalli ta tarayya da kungiyar tarayyar Turai da kuma shirin yaki da sauyin yanayi na gwamnatin Nigeria bisa kawo shirin yaki da sauyin yanaya nan jihar Kano, wanda a cewarsa hakan yayi dai-dai da kudirin gwamnatin jihar Kano ya yaki da matsalar.

Dakta Kabiru Getso ya ce shirin zai samar da hanyoyi da fasaha da kirkire-kirkire da bunkasa tsaftar muhalli da hanyoyin kula da muhalli mai dorewa da tattaunawa da masu ruwa da tsaki a bangaren kula da muhalli da shugabannin alumma da nufin aiwatar da tsare-tsaren da zasu kawo cigaban muhalli a fadin jihar Kano.

Ku Karanta: Tsaftar Muhalli: Mun Sauya Tsarin Aiki Zuwa Duba Guraren Samar da Abinci ga Al’umma — Kabiru Getso

A jawabinsa, shugaban ayarin shirin yaki da sauyin yanaya na gwamnatin tarayya Dakta Todd Ngara ya ce taron ya mayar da hankali wajen wayar da kan jamaa game da illolin sauyin yanayi inda yake tattaunawa da kungiyoyi masu zaman kansu da masu yin dokoki [Yan Majalisu] da shugabannin alumma da  kuma matasa domin isar da sakon yaki da sauyin yanayi a kasar nan.

Dakta Todd Ngara ya kuma yabawa gwamnatin jihar Kano bisa samar da tsare-tsare da dokoki da zasu bada gudun mowa domin samun nasarar da aka sanya a gaba.

Leave a Comment