Kasuwanci

Matsalar mu Shine Gwamnatoci Basa Tallafawa Masu Safarar Shanu — Mustapha Ali

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Ibrahim Sani Gama

Kungiyar masu fataucin shanu da dabbabi ta kasa, ta bayyana nasarari da kalubule da ta fuskanta a wannan lokaci na wannan sabuwar shekara da muka shigo ta 2023.

Shugaban kungiyar na kasa Alhaji mustapha Ali ne, ya bayyana haka a zantawarsa da manema labarai dangane da shigowar sabuwar shekara da muke ciki, da yadda alumma suke ciki a halin yanzu.

Shugaban ya ce, kungiyar masu fataucin shanu ta fuskanci matsaloli da suka hadar da, rashin cikakkiyar kulawa a fannin harkokin tsaron yan kungiyar kasancewar sun samu cin mutunci da wasu suka rika yiwa ‘ya ‘yan kungiyar dake safafarar shanu da dabbobi zuwa yankunan kudancin najeriya, amma sun tafka mutukar asara ta miyoyin kudade Wanda kuma babu wani taimakon da suka samu daga mahukunta ko Gwamnatoci.

Ya kuma ce rashin ci gaban tattalin arziki ya janyowa harkokin kasuwancinsu na fataucin shanu da dabbobi koma baya da tasgaro,Wanda da yawa matasan da suke cin Abinci ta wannan sana’a suna cikin damuwa kuma Gwamnatin tarayya ta ki bin hanyoyin da za ta taimakawa wadannan irin mutane dake bukatar agaji Wanda say da yawa shike haifar da rikice rikicen zai fara run daga karami ya zama babba,Wanda ba fatan haka ake ba.

Ku Karanta: Bamu Ji Dadin Tsarin Takaita Cire Kudin Da CBN Ya Kawo Ba — Kungiyar Masu Safarar Dabbobin

Mustapha Ali ya jaddada cewa,daga cikin manya nasarorin da kungiyar masu fataucin shanu da dabbobi ta kasa,ta samu,akwai, dakatar da yunkurin da Gwamnan Adamawa na kara kudaden haraji ga masu fataucin shanu da dabbobi na jihar da tallafawa marayu ‘ya’yan yankungiyar suka rasu suka bari,da tallafin jari ga yankungiyar a shiyoyinta na jihohin Najeriya.

Shugaban yace, kungiyar a shirye take wajen baiwa duo sani shugaba ko dantakara da zai jibirinci lamarin kungiyar masu fataucin shanu da dabbobi da yankungiyar, wajen tallafa musu da kayayyakin da za su bunkasa harkokin kasuwancinsu,da samarwa alumma da matasa sana,oin dogaro da kawunansu.

Ku Karanta: Mun Shirya Ceto Kano, Inganta Kasuwanci Da Gina Al’umma Idan Mukayi Nasarar Cin Zabe — Tanko Yakasai

Daga nan shugaban ya ja hankalin matasa da su kaucewa shiga bangar siyasa ko yin amfani da su wajen aiwatar da magudi ga wasu, inda ya ce, kamata yayi si Samar da nagartattun shugabanni da suke da kyakyawan tsammanin kawowa alumma ci gaba mai dorewa duba da halin da ake ciki a yanzu.

Leave a Comment