Siyasa

Matasa Suyi Riko Da Sana’ar Hannu Don Dogaro Da Kansu – Sanata Barau

Daga: KABIR GETSO

Zababben Sanatan Arewacin Kano kuma mataimakin shugaban Majalissar Dattijan Nijeriya ta 10 Sen Barau I. Jibrin CON yayi kira ga dumbin matasan Nijeriya akan suyi ruko da Sana’ar hannu don dogaro da kansu.

Sanatan yayi wannan kiranne yayinda ya karbi bakuncin mambobin kungiyar kano State Consultative Forum a ofishinsa dake Abuja a ranar Juma’ar data gabata.

Sanatan yace tabbas a rayuwar matashi yanzu babu abunda yafiye masa samada yayi ruko da Sana’a kowace irice wadda yafi kwarewa akanta, saboda zakaga kowane gida suna da sana’ar dasuka gada kuma idan mutum yataso iyayensa zasu koyar dashi sana’ar, misali wasu zakaga gadon gidansu sana’ar kira suke, wasu kuma zakaga sana’ar mahauta ce, wasu kuma zakaga sana’ar rini, haka-zalika zakaga wani gidan Yan kasuwane wasu kuma sana’ar saka dadai sauransu.

Ya kara da cewa matasanmu na yanzu sunyi sake da wannan sana’o’in, tabbas indai matashi a yanzu yayi ruko da sana’arsa yadda yakamata yana samun ragin radadi wannan matsin da muke ciki”.

Shima a nasa Jawabin Mataimakin na Musamman ga sanatan a bangaren Daukar hoto Abubakar Jafar Tijjani ya bayyanna hakan a Matsayin wani yanayi da ya zama wajibi ga al’ummarmu da suyi amfani da wannan shawara ta sanatan domin tabbas sana’a tana taka muhimmiyar rawa wajen ganin nasarar matashi kuma zaka sameshi mai dogaro dakansa a koda yaushe.

Leave a Comment