Kasuwanci

Matasa Ku Guji Shiga Ayyukan Bata Gari — Kwamared Rabi’u Tumfafi

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Ibrahim Sani Gama

Shugabanni Kungiyar Kasuwar sayar da abinci da Dawanau a Karamar hukumar Dawakin Tofa sun bukaci matasa da su guji shiga kungiyoyin Bata Gari da kuma rike kananan sana’o’in dogaro da Kai.

Sakataren kungiyar kuma Garkuwar matasan Arewacin kasar nan, Kwamared Rabiu Abubakar Tumfafi ne ya bukaci hakan yayin bikin nada shi a matsayin Garkuwar matasan Arewacin kasar nan, Wanda kungiyar wayar da kan matasa ta arewa ta yi masa, tare da bashi lambar girmamawa wanda ya gudana a nan Kano.

Tumfafi ya ce, yanzu lokaci ya sauya da ya kamata matasa su zamto masu neman na kansu domin zama jakadu na gari a cikin alumma, ta yadda za’a yi alfahari da su a ko ina a fadin Duniya.

Kwamared Tumfafi ya ce rashin yin sana’a duk kankantarta yana daga cikin abubuwan da suke
Haifar da shiga munanan ayyuka da suka hadar da sace-sace da kwacen wayoyi Wanda ya kan kai ga har su raunata mutum.

Ya kuma shawarci yan kasuwa musamman da Gwamnati da masu ruwa da tsaki da masu hannu da shuni da su tallafawa matasa wajen ganin sun samu sana’o’in da zasu dogara da kansu, domin kaucewa munanan dabiu.

Ku karanta: Gwamnatin Kano Za ta Nemi Tallafin Bankin Duniya Don Gina Dam-dam Uku

A jawabinsa, shugaban kungiyar wayar da Kan matasan Arewacin kasar nan, sanata Usama Galadima wanda kakakin kungiyar, Ambasada Mahmud Sa’id, ya wakilta, ya ce kuginyar ta karrama Abubakar Tumfafi ne, bisa jajircewar da yake da ita da tallafawa matasa da dalibai wajen ganin sun dogara da kawunansu ta fannoni da dama da biya musu kudaden karatu da sauran abubuwa.

Daga nan ya bukace su daya yi amfani da wannan dama domin ci gaba da wayar da kan matasa da tallafa musu a koda yaushe domin su zamto manyan jakadu na gari a jihar nan da ma kasa baki daya.

Da yake Karin haske ga matasa da daliban kasar nan, Kwamishinan kimiyya da fasaha na jihar Kano, Alhaji idris Garba, ya bukaci kungiyar da ta kara zage damtse wajen ganin ta ci gaba da wayar da kan matasan Arewacin kasar nan, ta yadda zasu yi amfani da wayoyin hannu da naura mai kwakwalwa wajen samarwa kawunansu abubuwan yi da za su dogara da su, kasancewar ayyukan yi sun yi karanci.

Ku Karanta: Zamu Cigaba da Bawa Gwamnati Hadin Kai Don Kwashe Sharar Kano — Kungiyar Direbobin Tifa

Kwamishinan ya ce wayoyin hannu, ba wai kawai za, a yi amfani da su bane wajen sada zumunci kadai ba, har ma da samar da ayyukan yi a zamanance.

Haka zalika, ya kara da cewa, Gwamnatin jihar Kano, ta kafa cibiyar koyan Sana’o’in dogaro da Kai a hanyar Zaria ga daliban da suka kammala karatu basu samu aiki ba, inda ya ce, cibiyar tana koyar da sana’o’i daban daban domin rage marasa ayyukan yi.

Ya kuma shawarci, Kwamared Rabiu Abubakar tumfafi, daya kara himma wajen tallafin daya saba yi, domin irin jajircewar da yake da ita da gudunmawar da yake bayarwa ga matasan kasar nan, ya sanya suka nadashi a wannan matsayi.

Garkuwan ya godewa Allah subhanahu wataala bisa nadin nasa, ya kuma bayyana cewa zai cigaba da yin duk Mai yuwuwa domin cigaban al’umma.

Daga nan ya godewa majalisar wayar da kan matasan Arewacin kasar nan bisa karamcin da suka yi masa, inda yayi musu fatan alheri tare da adduar samun nasara a dukkannin manufofin su.

Leave a Comment