Da Dumi-Dumi

Mataimakin gwamnan jihar Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya Kai ziyarar Ta’aziyya wasu yankunan Jihar nan

By: SHEHU SULEIMAN SHARFADI

Mataimakin gwamnan jihar Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya Kai ziyarar taaziyya ga iyalan marigayi Alhaji Nura Danjani hadejia a unguwar hausawar fulani dake karamar hukumar Tarauni wanda ya rasu a jiya.

Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya kwatanta rasuwar Alhaji Nura Danjani a matsayin gagarumin rashi ba ga iyalansa kadai ba har ma da daukacin al’ummar musulmin Jihar nan.
Mataimakin gwamnan ya yi wa marigayin fatan samun rahamar Allah tare kuma da baiwa iyalansa hakurin jure rashinsa.

Kazalika mataimakin Gwamnan Jihar nan Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya Kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Garba Magashi wanda shahararren malami ne a Jihar Kano.

Marigayi Alhaji Garba Magashi wanda ya rasu a jiya mahaifi ne ga Dakta Aminu magashi wanda kwararren likitane a jihar nan.

Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo yayi masa fatan samun rahamar Allah tare da baiwa iyalansa hakurin jure rashinsa.

Leave a Comment