Yanzu-Yanzu

Mata sun samu tallafi daga kungiyar tallafawa mata – Ambs. A’isha

By: Kabir Getso

 

 

kungiyar tallafawa mata don dogaro da kai wato (women intuitive for Family Economy)
karkashin jagorancin Shugabar kungiyar Hajiya Amb A’isha Abdulkadir.

Inda mata da dama suka sami horo gami da tallafin kayayyakin sana’ar wadanda suka hada da kekunan dinki,firinji da sauran kayayyki harma daya daga cikin wacce ta amfana da tallafin tayi mika sakon godiya ga kungiyar

shima dan takarar Majalisar Dattijai mai wakiltar Kano ta Tsakiya a jam’iyyar APC Hon Abdulkarim AA zaura ya yabawa wannan kungiya bisa wannan gagarumin Gudummuwa da take bawa mata,inda yaja hankalin mata da su jajurce wajen adana kayayyakin sana’ar tasu don cin moriyar abin.

Bugu da gari A A zaura ya bawa wannan kungiya Gudummuwa na kekunan dinki da sauran kayayyki da kuma kudi Naira Miliyan 3 don cigaba ta tallafwa matan jihar kano

Itama Shugaban Kungiyar ta WIFE Hajiya Amb A’isha Abdulkadir ta yabawa matan bisa amsa gayyatar taron tare da kira garesu su da sucigaba da bawa kungiyar hadin kai don samun Cigaban kungiyar,tare da roko garesu da su zabi jam’iyyar APC a dukkanin zabuka masu zuwa.

taron ya samu halartar manyan mutane na ciki da wajen jihar kano Mata da maza.

 

 

 

Leave a Comment