Da Dumi-Dumi

Masarautar Kano Ta Ja Hankalin Iyaye Akan Kula Da Karatun ‘Ya’yansu

Written by Pyramid FM Kano

Daga: JAMILA SULEIMAN ALIYU

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira ga iyaye akan su ringa baiwa ilimin ‘ya’yansu mahimmanci awani bangare na bikin ranar yara da ake cigaba da gudanarwa a makarantu masu zaman kansu na daga cikin masu gudanar da bikin.

Hajiya Maryam Hameed tace, sunga dacewar gudanar da taro ta hanyar gayyato yara ‘yan mmakarantu masu zaman kansu da na gwannatin ma domin gudanar da murna a tare tare da jan hankalin yaransu dage da karatunsu saboda su kai matakin da ake musu fata na zama manyan gobe.

Haka zalika, ta bayyana cewa taron hanyace ta sa farin ciki da nishadi ga yaran ta yadda zasu san Suma suna da mahimmanci a tsakanin al’umma.

Shugabar makarantar Ogba Comprehensive Hajiya Surayya Husain Lawan wadda Malam Salim Jabir Malami Mai jawabi a madadinta yace, Maimartaba Sarkin Kano da Malam Shekarau sun cancanci yabo bisa yadda suka baiwa taron Mahimmanci kuma suka ja hankalin yaran wasu yaran da Pyramid FM ta zanta dasu sun bayyana jin dadinsu bisa wannan gagarumin taro da aka shirya don su.

Leave a Comment