Addini Da Dumi-Dumi

Majalisar Shura Ta Darikar Tijjaniya Ta Nuna Rashin Goyon Bayan Matakin Soja Ga Nijer – Inyas Abubakar

Daga: MUKHTAR YAHAYA SHEHU

Majalisar shura ta Darikar Tijjaniya ta nuna rashin goyon bayan matakin soja a Kasar ta Nijer.

Majalisar ta sanar da haka ne cikin takardar bayan taron Zikirin Shekara da ta saba gudanar wa a fadar Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ranar Juma’a 24 ga watan Muharram 1445 bayan Hijra wacce ta yi daidai da 10 ga watan Ogustan 2023. Mai dauke da sa hannun shugaba da sakataren yada labaran kwamitin wato Ibrahim Inyas Abubakar da kuma Abubakar Balarabe Kofar Na’isa.

1. Taron yayi kira ga al’ummar Musulmi su maida hankali wajan yin addu’o’i domin warwarewar matsalar tsaro da ake fama da ita a wasu sassa na Kasar nan da kuma tsadar rayuwa da ake ciki yanzu.

2. Taron ya nuna kyamarsa da kin amincewa wajan yin amfani da karfin Soja, wajan warware matsalar Kasar Nijer, maimakon haka a cigaga dayin amfani da hanyar Difilomasiyya kasancewar Nijeriyya da Nijer duka abu daya ne.

3. Taron yayi kira ga Hukumomi su tashi tsaye wajan magance matsalolin shaye-shaye ga Matasa, rashin aikinyi da magance ayyukan ashsha da ake fama dasu daga bangaren matasa.

4. Taron yayi bayani akan irin yadda sufanci ya bada gudunmawa wajan yada ilimin addinin Musulunci tareda karantar da ingantacciyar fahimtar addinin Musulunci da yada zaman lafiya a tsakanin al’umma.

5. Kazalika taron ya bukaci Gwamnati a kowanne mataki su tallafawa al’umma domin rage radadin halin matsi da al’umar Kasar nan suke ciki.

6. Taron yaja hankalin iyaye akan su tsaya ga abunda ya zama wajibi akansu na tarbiyar ‘yayansu da kiyaye lafiyarsu, Mutuncinsu da karesu daga fadawa cikin miyagun ayyuka.

7. Haka kuma an bukaci al’umma su koma zuwa ga Allah da yin tuba da kamewa daga barin laifuka wadanda Allah ya hana, kyautata mu’amulla a tsakanin juna, tausayawa na kasa, domin yin hakan Allah zai dubemu da rahamarsa ya yaye mana halin da muke ciki.

8. Taron ya tsawatar wa masu fassara littattafan magabata da ra’ayin su ba tare da sanin abinda mawallafan suke nufi ba, domin kaucewa batanci ga marubutan da kuma dora Al’umma aka gurbatacciyar fahimta.

9. Taron kazalika yayi kira ga mabiya Darikar Tijjaniyya su cigaba da aiki da koyarwar Shehu Ahmadu Tijjani (RA) da Shehu Ibrahim Inyass (RA) suka dorasu akai.

10. Taron daga karshe yayi addu’a ga shugabanni akan Allah yayi ruko da hannayensu yayi musu jagoranci kuma yasa tausayin Al’uma a zukatansu.

Leave a Comment